Gwamnatin Tinubu Ta Ce Ta Tarar Da Tattalin Arziƙi Ƙasa Cikin Mummunan Yanayi
- An bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta tarar da tattalin arziƙin ƙasa a cikin mummunan yanayi
- Ministan kuɗi da tattalin arziƙin ƙasa Mista Wale Edun ne ya bayyana hakan bayan taron FEC
- Ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta riƙa ciyo bashi domin tafiyar da harkokin ƙasa ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta tarar da tattalin arziƙin ƙasa a cikin mummunan yanayi da kuma matsanancin rashin aikin yi.
Ministan kuɗi da tattalin arziƙin ƙasa Mista Wale Edun ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kamalla taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Halin da Tinubu ya tarar da tattalin arziƙin ƙasa
Wale ya shaidawa manema labarai cewa shugaba Bola Tinubu ya karɓi ƙasar nan ne a lokacin da tattalin arziƙinta ya shiga wani mummunan hali gami da rashin aikin yi.
Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce a yayin taron da ya gudana ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, sun tattauna batun rashin aikin yi na matasa da kuma batu na tsadar rayuwa da 'yan ƙasa suke ciki kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba za ta riƙa ciyo bashi domin gudanar da ayyuka ba, sai dai za ta yi ƙoƙarin janyo masu zuba hannayen jari na cikin gida da na waje.
Tinubu ya nemi ministocinsa su ankarar da shi a yayin da ya yi kuskure
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan roƙon da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ministocinsa a sha'anin gudanar da shugabancinsa.
Shugaba Tinubu ya roƙi ministocin na sa da su yi ƙoƙarin ankarar da shi a duk lokacin da suka ga yana neman kauce hanya tunda a cewarsa shi ɗan adam ne ajizi.
Hannatu Musawa Tana Bukatar NYSC Satikifet Domin Zama Minista? Babban Lauya Ya Bayyana Yadda Lamarin Yake
Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar zartarwa na farko da ya gudanar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin, 28 ga watan Agusta a fadar gwamnati da ke Abuja.
Mutane sun fasa rumbun ajiyar abinci na jihar Bayelsa
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan farmakin da mutane suka kai wa rumbun ajiyar kayan abinci na tallafi a jihar Bayelsa da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.
Hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA) a jihar ta Bayelsa, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutane sun ɗibi abincin duk kuwa da cewa ya riga da ya fara ruɓewa.
Asali: Legit.ng