Shugaba Tinubu Zai Kori Duk Ministan Da Bai Yi Abinda Ya Dace Ba, Inji Ajuri Ngelale

Shugaba Tinubu Zai Kori Duk Ministan Da Bai Yi Abinda Ya Dace Ba, Inji Ajuri Ngelale

  • An bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai lamunci gazawa daga ministocinsa ba
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a ranar Litinin
  • Ya ce Tinubu ya tsarawa kowane minista aikin da zai yi kuma ba zai ji tsoron korar duk wanda ya gaza ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - An bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a shirye yake ya fatattaki duk wani ministan da bai yi abun kirki ba.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a yayin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels.

Tinubu ba zai lamunci gazawa daga ministocinsa ba
Shugaba Tinubu zai kori duk ministan da bai yi abinda ya dace ba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu zai kori duk ministan da bai yi abinda ya dace ba

Ajuri Ngelale ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai lamunci gazawa daga kowane daga cikin ministocinsa ba tunda ya bai wa kowanensu aikin da yake so ya yi.

Kara karanta wannan

Ba Za Ta Yi Wu Ba: Tinubu Ya Bayyana Tsari 1 Na Buhari Da Ba Zai Cigaba Da Shi Ba

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce shugaban ya shafe duka watannin da ya yi bayan zaɓe, wajen tsarawa kowace ma'aikata aikin da ya dace da ita.

Ngelale ya kuma ce idan aka yi la'akari da yadda ya gudanar da mulkinsa lokacin da yake gwamnan Legas, za a ga cewa Shugaba Tinubu ba zai ji tsoron korar duk wani ministansa da bai yi abinda ya dace ba.

Ya ƙara da cewa Tinubu zai tabbatar da cewa ministocin sun yi abinda ya kamata, saboda idan suka gaza shi za a zarga ba ministocin ba kamar yadda PM News ta wallafa.

Tinubu zai ƙarasa ayyukan da Buhari ya fara

Ngelale ya kuma bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai ɗora daga kan wasu ayyukan da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi, musamman ma waɗanda ya aiwatar cikin nasara.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Tsohon Shugaban EFCC Bawa Damar Ganin Lauyoyi Da Yan Uwansa

Ya ƙara da cewa gwamnatin ta Tinubu za ta bai wa kowane minista wa'adi domin ya kammala duk ayyukan da aka ba shi, wanda da wannan ne za a riƙa auna ƙoƙarinsa.

Ngelale ya kuma ce wannan ne karo na farko a tarihin Najeriya da ake sanyawa kowane minista wa'adi wajen aiwatar da abinda ake so ya yi.

Tinubu ya ce ba zai ci gaba da kwashe kudi yana biyan bashi ba

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan iƙirarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na cewa ba zai ci gaba da tsarin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗora ƙasar a kai ba.

Tinubu ya ce ɗabi'ar nan ta biyan bashi da kusan kaso 90% na kuɗaɗen ƙasa da ake yi a baya, ba za ta ci gaba da wanzuwa a gwamnatinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng