Jigon Jam'iyyar APC Ya Yabawa Shugaba Tinubu Bisa Gwangwaje 'Yan Kabilar Ibo Da Manyan Ministoci

Jigon Jam'iyyar APC Ya Yabawa Shugaba Tinubu Bisa Gwangwaje 'Yan Kabilar Ibo Da Manyan Ministoci

  • An yabawa Shugaba Tinubu bisa gwangwaje ƴan ƙabilar Ibo da muƙamai masu gwaɓi na ministoci a gwamnatinsa
  • Jigon jam'iyyar APC, Okoye Francis ya bayyana cewa ma'aikatun da Shugaba Tinubu ya ba ƴan ƙabilar Ibo ya nuna cewa yana son yankin Kudu maso Gabas
  • Yayin tattaunawa ta musamman da Legi.ng, Okoye ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ƙara naɗa wasu ministoci biyu daga yankin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam'iyyar APC a yankin Kudu maso Gabas, Okoye Francis, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa ba ministoci ƴan ƙabilar Ibo ma'aikatu masu gwaɓi.

Okoye ya bayyana cewa wannan ne karon farko da ministocin da suka fito daga yankin Kudu maso Gabas za su jagoranci manyan ma'aikatu guda huɗu.

Jigon APC ya yabawa Shugaba Tinubu
Jigon APC ya yabawa Shugaba Tinubu bisa bayar da yankin Kudu maso Kudu ministoci masu gwabi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu yana son mutanen yankin Kudu maso Gabas

Kara karanta wannan

"Ba Zai Yiwu Ba": Sojojin Nijar Sun Bayyana Dalilin Kin Dawo Da Bazoum Kan Mulki

A wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng, Okoye ya bayyana cewa naɗin muƙaman ya nuna shugaban ƙasa Ɓola Tinubu yana son mutanen yankin Kudu maso Gabas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Ina son na yabawa shugaban ƙasa saboda wannan ne a karon farko a cikin ministoci biyar daga yankin Kudu maso Gabas, muka samu manyan ministoci guda huɗu, inda ɗaya daga cikinsu ne kawai ƙaramin minista, Nkiruka Onyejiocha, wanda aka ba ƙaramin ministan ƙwadago."
"Ragowar manyan ministoci ne wanda hakan shi ne karon farko a tarihin ƙasar nan."
"Muna da ɗan ƙabilar Ibo a matsayin ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, hakan bai taɓa faruwa ba a tarihin ƙasar nan, ɗan ƙabilar Ibo ya riƙe wannan ma'aikatar mai matuƙar muhimmanci."

Ƙarin ministoci 2 ga yankin Kudu maso Gabas

Ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya duba yiwuwar ba mutanen yankin Kudu maso Gabas ƙarin ministoci biyu.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Tarbi Wakilan Amurka, Ya Bayyana Sabbin Bayanai Kan Matsayar ECOWAS

"Mutanen yankin Kudu maso Yamma suna da ministoci tara, Arewa maso Yamma suna da ministoci 10, Kudu maso Kudu suna da takwas, Arewa ta Tsakiya suna da takwas. Yankin Kudu maso Gabas ne kawai yake da ministoci biyar." A cewarsa.
"Hakan na nufin kowacce jiha na da minista ɗaya a gaba ɗaya yankin Kudu maso Gabas, wanda hakan ba adalci ba ne."

Tinubu Ya Fadi Abinda Yake So Wike Ya Yi

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyanawa ministan birnin tarayya Aɓuja, Nyesom Wike, abin da yake so ya cimmawa a birnin.

Sjugaba Tinubu ya bayyana cewa yana son Wike ya kammala aikin jirgin ƙasa na birnin Abuja da aka daɗe ba a kammala ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng