Kano: Ana So Ayi Amfani da Kotu, A Tsige NNPP a Dawo da APC - Malamin Addini
- Dr. Sani Ashir ne wanda ya jagoranci sallar da gwamnatin Kano ta shirya domin kawo zaman lafiya
- Malamin ya zargi wadanda ya kira makiyan jihar Kano da kutun-kutun domin a dawo da APC kan mulki
- Ana shirin amfani da kotun karar zabe da nufin ruguza nasarar NNPP a zaben Gwamna da aka yi
Kano - Wani malamin addinin musulunci a jihar Kano, Sani Ashir ya ce wasu mutane su na son amfani da kotu domin dawo da jam’iyyar APC.
Dr. Sani Ashir ya kira wadannan mutane da makiyan Kano, yake nuna ana kokarin tsige NNPP daga kan mulki, Daily Nigerian ta fitar da rahoton.
Malamin ya yi wannan bayani ne yayin da ya jagoranci sallar ta gwamnatin jihar Kano ta shirya da sunan Allah (SWT) ya kawo saukin rayuwa.
Sallah ta musamman a Kano
An yi sallah raka’a biyu a Filin Mahaha da ke garin Kano a ranar Asabar ganin halin da ake ciki na tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci a yau.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Aminu Abdulsalam da manyan gwamnati sun halarci sallar tare da Rabi’u Musa Kwankwaso.
A lokacin da yake addu’a, sai aka ji Sheikh Sani Ashir ya na rokon Allah (SWT) ya yi wa Kanawa tsari daga wasu da ya ce makiya jihar Kano ne.
Jam'iyyar NNPP za ta rasa Gwamnati?
Malamin da ya samu mukami da NNPP ta karbi mulki ya zargi wadannan mutane da shirya yadda za su ga bayan jagororin gwamnatin jihar Kano.
An rahoto Dr. Ashir ya na cewa makiyan sun dage ido rufe da nufin ruguza nasarar da jam’iyyar NNPP ta samu ta hanyar kuri’un al’umma a zabe.
Nasara a Kotun Zabe: Kwankwaso, Abba Gida Gida Da Wasu Jiga-Jigan NNPP Sunyi Taron Addu’a Na Musamman a Kano
A duk inda su ke, malamin musuluncin ya roki Ubangiji Madaukakin Sarki (SWT) ya rusa wadanda ya dace su na so kuri’un mutane su bi iska.
Sannan malamin ya roki Allah (SWT) ya birkita abokan adawar gwamnati mai-ci, tare da kawo dawamammen zaman lafiya da kuma cigaba.
"An samu cigaba a Kano a mulkin NNPP"
Kafin a bar musallar, limamin ya jero amfanin da aka samu a karkashin gwamnatin Abba Yusuf tun daga gyaran ruwa zuwa, kasuwanci da ilmi.
An dawo da fitilun titi, ana gyara asibitoci da kawo kayan aiki, ana gyara makarantu, za ayi auran zaurawa, bayan taimakawa dalibai da kai wasu waje.
Asali: Legit.ng