Tinubu Ga Yan Najeriya: Ku Canza Gwamnonin da Suka Gaza Yin Aiki

Tinubu Ga Yan Najeriya: Ku Canza Gwamnonin da Suka Gaza Yin Aiki

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya su canza duk gwamnan da ya gaza yin abinda ake tsammani
  • Shugaban ƙasan ya ce ba shi da hurumin bai wa gwamnoni umarni amma zai yi kira da su raba tallafin da aka ba su ga jama'a
  • Ya faɗi haka ne yayin da wasu Malamai suka roƙi ya sanya ido kan yadda jihohi zasu raba tallafin rage raɗaɗi da FG ta basu

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su canza gwamnonin da ba su yi aikin da ake tsammani ba idan babban zaɓe ya zo.

Shugaban ya yi wannan kira ne ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja yayin da yake martani kan buƙatar wasu malaman Addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Ana tsaka mai wuya: Abin da Tinubu ya fadawa Malaman addini kafin su tafi Nijar

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tinubu Ga Yan Najeriya: Ku Canja Gwamnonin da Suka Gaza Yin Aiki Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Malaman sun buƙaci gwamnatin tarayya ta sanya ido kan yadda ake rabon kayan agajin da aka bai wa jihohi domin dakile illolin cire tallafin man fetur.

Tinubu ya ce ba zai iya ba jihohi umarni ba saboda sun fi kusanci da jama’a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abinda zan iya faɗa wa gwamnoni - Tinubu

A cewar shugaban ƙasar, abinda zai iya kawai shi ne ya yi kira ga gwamnoni su aiwatar da umarnin da aka ba su dangane da rabon kayan tallafi domin rage wa yan Najeriya radaɗi.

Haka nan kuma shugaba Tinubu ya bayyana cewa ƙanana da matsakaitan sana'o'i zasu samu karin tallafi daga gwamnatin tarayya.

A kalamansa ya ce:

“Mutane suna rayuwa ne a cikin jihohi. Ko da na kafa kwamiti sai na bi ta hannun gwamnoni da kananan hukumomi. Za mu ci gaba da tattaunawa da gwamnoni, ya zama tilas yan Najeriya su sa ido kuma su tuhume su."

Kara karanta wannan

Tallafin Biliyan 5: Tinubu Ya Fadi Abin Da Zai Yi Don Tabbatar Da Adalci A Rabon, Ya Roki Gwamnoni

“Babu haka a tsarin mulkin dimokradiyya; shugaban kasa na zaune a nan yana bada umarni ga jihohi. Abinda zan iya kaɗai shi ne kira gare su da su aiwatar."
"Mutane na zaune suna rayuwa a jihohi, idan kuma gwamna ya gaza yin abinda ya kamata, ya zama dole mutane su sauke shi daga mulki."

FG ta yi tanadin kuɗin da ya kai Naira biliyan 5 ga kowace jiha domin dakile tasirin cire tallafi amma ana fargabar cewa wasu gwamnonin na iya gurɓata tsarin, Daily Post ta rahoto.

Shugaba Tinubu ya gana da Wike a Villa

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu da Ministan babban birnin tarayya sun yi ganawar sirri a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis.

Duk da ba a bayyan dalilin wannan taron ba amma ana hasashen ba zai rasa nasaba da rushewar benen nan da ya faru ba.

Kara karanta wannan

Ana Wahala: Malamin Addinin Musulunci Ya Roki Gwamna Ya Kawowa Talaka Agaji Bayan Tallata APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262