Wike: Shehu Sani Ya Ƙalubalanci Atiku Da PDP Kan Ci Gaba Da Shari'a Da Tinubu
- 'Yan Najeriya da dama dai ma ganin cewa ƙarfin jam'iyyar PDP ya ragu a siyasar ƙasar nan
- Sanata Shehu Sani ya yi martani kan damar da PDP ta bai wa wasu 'ya'yanta na shiga a dama da su a gwamnatin APC
- Ya ƙalubalanci jam'iyyar ta PDP kan ci gaba da shari'a da Tinubu duk da abinda ya faru
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi martani kan karɓar muƙamin da Nyesom Wike ya yi a gwamnatin Tinubu duk da kasancewarsa ɗan PDP.
Tsohon gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike dai yana cikin minstoci 45 da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a matsayin waɗanda za su taya shi aiki a gwamnatinsa.
Shehu Sani ya ƙalubalanci Atiku da PDP kan Shari'a
Biyo bayan karɓar muƙamin minista da Wike ya yi, 'yan Najeriya da dama sun yi tsokaci kan ƙarfin da jam'iyyar adawa ta PDP take da shi a yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Nyesom Wike jim kaɗan bayan karɓar rantsuwar fara aiki, ya yi iƙirarin cewa sai da ya samu amincewar jam'iyyarsa ta PDP kafin ya karɓi muƙamin ministan da aka ba shi kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Da yake martani kan muƙamin da Wike ya karɓa a gwamnatin Tinubu, Sanata Shehu Sani ya ce babu buƙatar PDP ta ci gaba da zuwa kotu tana ƙalubalantar sakamakon zaɓe tun da ɗan ta ya karbi muƙami.
Ya wallafa saƙon ne a shafinsa na X kamar haka:
Martanin masu amfani da X ga Shehu Sani
Mutane da dama da ke bibiyar Shehu Sani a shafin X sun tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan saƙo da ya wallafa. Ga wasu daga cikinsu kamar haka:
@MyrorMiller ya ce:
“PDP a haka dai sun bar Atiku kaɗai da zuwa kotu, kuɗin da ya ba su sun ƙare kuma ya ƙi ƙara mu su wasu, sun tsallake jirgin na sa.”
@007_Increadible ya ce:
“Ina ganin jam'iyyarsu ce ta fi kowace ruɗewa a halin da ake ciki, ko jam'iyyar su Kwankwaso sun fi su maida hankali kan abubuwan da suka sa gaba.”
“Koda yake lokacin kamfen mun ji wani abu wai ‘PDAPC’, ba mamaki hadakar da aka yi ce take bayyana a hankali a hankali.”
@FESTUSSMART5 ya ce:
“Wike shi kaɗai ne a PDP din da yake ciki. Ba ya da wata alaƙa da uwar jam'iyya ta ƙasa.”
An zargi Tinubu da neman ɓatawa Atiku suna
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan zargin da wata kungiya mai suna Face of Waziri-Nigeria (FOWN) ta yi na cewa Shugaba Tinubu na neman ɓatawa Atiku Abubakar suna.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa Tinubu na yunƙurin ɓata sunan Atiku ne biyo bayan wata ƙara da ya shigar kansa a wata kotu da ke ƙasar Amurka.
Asali: Legit.ng