Ministocin Bola Tinubu Za Su Lakume Kusan Naira Biliyan 9 Kafin Su Bar Ofis a 2027
- Bola Ahmed Tinubu ya kafa gwamnatin da ta fi kowace yawan ministocin tarayya a tarihin Najeriya
- Ministoci 48 za su yi aiki da shugaban kasar, kowanensu ya na da albashi mai tsoka a kowane wata
- A cikin shekaru hudu, babu mamaki gwamnatin APC mai-ci tayi barnar abin da ya zarce N8bn
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Nan da shekaru hudu masu zuwa, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta kashe kudin da ya zarce Naira biliyan takwas a kan ministocin tarayya.
Wani bincike da Daily Trust ta gudanar, ya nuna Najeriya za ta batar da Naira biliyan 8.63 domin biyan albashi, alawus da duk sauran hakkokin ministocin.
Abin bai tsaya nan ba, ana zargin kudin zai iya karuwa idan har hukumar RMAFC ta yi wa masu rike da mukamai karin albashi a kan abin da su ke karba.
Hakan ya nuna tafka da warwarar shugaba Bola Tinubu mai kokarin rage facaka da dukiyar al’umma, ana fito da tsare-tsare domin rage radadin talauci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ministoci za su karbe albashin N13bn
Rahoton ya tabbatar da cewa ministocin da za su nada hadimai barkatai, za su sake jefa tattalin arziki cikin matsala, a rika batar da miliyoyi a duk wata.
Abin da za a kashe a wajen biyan albashi ga ministocin zai ci wa gwamnatin tarayya Naira biliyan 13. A haka ba a hada da manyan alawus da su ke ci ba.
...Dalar Amurka za ta kara karyewa
Sa'ilin da minista da mukarrabansa su ka bar Najeriya zuwa kasar waje, ana biyansu alawus a kudin ketare, hakan zai iya taimakawa wajen tashin Dala.
Hukumar RMFAC ta tsaida albashin minista a kowane wata a kan N650,135.99, a kowace shekara minista guda zai karbi N7.8m daga hannun gwamnati.
Lissafin Legit.ng Hausa ya nuna a albashi kawai, duka ministocin za su ci 37,447,833,024 duk shekara a lokacin da ake kukan abinci ya yi tsada.
Alawus da Minista yake karba
Daga cikin kudin akwai N1,519,800 domin hawa mota, N506,600 na sallamar mukarrabai, N1,519,800 domin barori sai kuma N911,880 na shakatawa.
Doka ta ba minista damar kashe N303,960 da sunan sayen jaridu. Bayan haka akwai kudin kama hayar gda, sayen kayan daki da motoci da kudin hutu.
Hakan ya nuna a shekaru hudu, ministocin da za su yi aiki da gwamnatin nan za su ci N1.497bn a duk wata tun da a shekara hudu za su tashi da N31.2m.
Akwai wani karin alawus na N37.28m da ake biyan ministoci, hakan zai bada damar kashe masu N1.785bn a shekara, za su batar da N7.142bn nan da 2027.
Ministoci 48 a FEC
A tarihi, tun daga Muhammadu Buhari, Goodluck Jonathan da Umar Yar’Adua, ba a taba samun lokacin da shugaban kasa ya rantsar da ministoci 45 ba.
Ku na da labari Bola Tinubu ya dauki aro a wajen tsohon shugaban kasar nan watau Muhammadu Buhari, bai ba kowa babbar kujerar Ministan fetur ba.
Asali: Legit.ng