Jerin Ministocin Shari'a, Antoni Janar da Aka Yi a Najeriya Tun Daga 1999
FCT Abuja - Ofishin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya na daya daga cikin ma’aikatun gwamnati da ke da matukar muhimmanci a Najeriya.
Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, hazikan ‘yan Najeriya tara ne suka riƙe ofishin a lokuta daban-daban.
Tsohon AGF da ya gabata, Abubakar Malami, shi ne ministan shari'a mafi daɗewa tun 1999 yayin da, Adetokunbo Kayode ke rike da tarihin zama minista mafi karancin lokaci.
Jerin ministocin shari'a kuma Antoni Janar tun daga shekarar 1999
A wani rahoto da @StatiSense ta wallafa a shafin Tuwita, mun haɗa muku jerin Ministocin Shari'a da Antoni Janar na Tarayyar tun daga 1999, ga su kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Kanu Agabi (1999-2000)
Agabi ya yi aiki a matsayin ministan shari'a kuma Antoni Janar a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Osinbajo.
- Bola Ige (2000-2001)
Ige ya gaji Agabi a matsayin AGF na ƙasa duk a ƙarƙashin mulkin Obasanjo.
- Kanu Agabi (2002-2003)
Obasanjo ya sake naɗa Agabi karo na biyu a wannan muƙami mai daraja a gwamnatin Najeriya a shekarar 2002.
- Akin Olujimi (2003-2005)
Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya naɗa Olujimi a matsayin ministan shari'a na uku a gwamnatinsa.
- Bayo Ojo (2005-2007)
Ojo shi ne mutum na karshe da ya riƙe kujarar ministan shari'a kuma Antoni Janar na tarayya a gwamnatin shugaba Obasanjo.
- Michael Aondoakaa (2007-2010)
Aondoakaa ya yi aiki a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Alhaji Umaru Musa 'Yar'adua.
- Adetokunbo Kayode - 2010
Kayode ya yi aiki a matsayin ministan shari'a a gwamnatin Yar'adua na tsawon mako biyar kaɗai.
- Mohammed Bello (2010-2015)
Yar'adua ya ƙara naɗa Mohammed Bello a matsayin ministan shari'a a 2010 gabanin ya rasu a cikin wannan shekara 2010.
- Abubakar Malami (2015-2023)
Malami ne ministan shari'a da ya fi kowanne daɗewa tun 1999 kuma ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
- Lateef Fagbemi (2023-Yau)
Fagbemi ne sabon Ministan shari'a kuma Antoni janar karƙashin gwamnatin shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu.
Peter Obi Ne Zai Yi Nasara a Kotu
A wani labarin kuma Wani fitaccen Malami addini ya bayyana wahayin da aka masa kan hukuncin da Kotun sauraron ƙorafin zabe zata yanke.
Fitaccen Malamin ya yi hasashen cewa kotun zabe (PEPC) zata rushe nasarar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , ya samu a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Asali: Legit.ng