Sanata Aduda Ya Samu Nasarar Zama Sabon Shugaban PDP Na Jihar Kogi
- Jam'iyyar PDP ta naɗa shugaban jam'iyya na rikon kwarya a jihar Kogi da Sakatare bayan karewar wa'adin zababbun mambobin NWC
- Sakataren tsare-tsare, Umar Bature ne ya sanar da haka, inda ya bayyana sunayen mambobin kwamitin rikon kwarya mai ɗauke da mutum 14
- PDP ta amince da naɗa tsohon sanatan Abuja, Philip Aduda a matsayin shugaban riƙo da kuma George Daika a matsayin Sakatare
Kogi state - Tsohon Sanata mai wakiltar mazaɓar birnin tarayya Abuja, Sanata Philip Aduda, ne zai jagoranci kwamitin riƙon kwarya na jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi.
Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Honorabul Umar Bature.
Sanarwan ta ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC-PDP) ga amince da kafa kwamitin riƙon kwarya mai ƙunshe da mutum 14 bayan tattaunawar neman shawari da masu ruwa da tsaki a jihar Kogi.
Bature ya bayyana cewa kwamitin, "Zai ci gaba da jan ragamar tafiyar da harkokin jam'iyyar PDP a jihar biyo bayan ƙarewar wa'adin zaɓaɓɓun mambobin NWC na Kogi."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jerin mutanen da suka shiga kwamitin riƙon kwarya
Sanata Aduda ne zai jagoranci kwamitin a matsayin muƙaddashin shugaban PDP reshen jiha yayin da Honorabul George Daika ya zama Sakataren jam'iyya.
Sauran mambobin kwamitin sun ƙunshi, Honorabul Joshua Adejoh, Sunday Shugaba, Paul Ukwenya, Honorabul Gbenga Olorunnipa, Honorabul MO Sule, Chief Dayo Akande da Honorabul Siyaka Uchunaye.
Audu Idris, Honorabul Sheidu O Abara, Bilkisu Onusagba, Abiola Olajubu da kuma Grace Atawodi duk suna cikin mambobin kwamitin rikon PDP a jihar Ƙogi da ke Arewa ta Tsakiya.
Nan gaba za a rantsar da kwamitin a ɗakin taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP ta ƙasa (NEC) wanda ke Wadata Plaza a babban birnin tarayya Abuja, Dailypost ta rahoto.
Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan jigon PDP ya shigar da ƙarar shugaban jam'iyya na ƙasa, Umar Damagun, NWC da NEC a gaban Kotu.
Shugaba Tinubu Zai Tsamo Yan Najeriya Miliyan 136 Daga Kangin Talauci
A wani rahoton na daban kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin tsamo yan Najeriya miliyan 136 daga ƙangin talauci da samar da ayyuka 10m.
Ministar harkokin jin ƙai da yaye talauci, Dakta Betta Edo ce ta bayyana haka yayin da ta shiga ofis a karon farko ranar Litinin.
Asali: Legit.ng