Cire Tallafi: Uba Sani Ya Rage Kudin Makarantun Gaba Da Sakandare a Kaduna

Cire Tallafi: Uba Sani Ya Rage Kudin Makarantun Gaba Da Sakandare a Kaduna

  • Gwamna Uba Sani ya sanar da rage yawan kuɗaɗen da ake biya a makarantun gaba da Sakandare na jihar Kaduna
  • Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin sauƙaƙawa 'ya'yan talakawa wajen yin karatunsu a jihar
  • A zantawarsa da Legit.ng, Dakta Alamuna Nuhu na jami'ar KASU, ya ce matakin zai rage yawan ɗaliban da ke barin makaranta saboda rashin kudi

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya sanar da rage yawan kuɗaɗen da ake biya a makarantun gaba da Sakandare na jihar.

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.

Uba Sani ya ragewa ɗaliban jihar Kaduna kuɗin makaranta
Gwamna Uba Sani ya zaftare kuɗin manyan makarantun Kaduna ga ɗalibai. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Uba Sani ya rage kuɗin manyan makarantu

Uba Sani ya dauki wannan matakin ne biyo bayan koken da al'ummar jihar suka shigar dangane da tsadar kuɗin karatu na manyan makarantun jihar.

Kara karanta wannan

“Ina Dalili”: Suka, Martani Kan Nadin Hadimai Mata 131 Da Gwamnan Arewa Ya Yi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wannan wani ƙoƙari ne na gwamnatinsa na ganin ta sauƙaƙawa 'ya'yan ma su karamin ƙarfi, wajen biyan kuɗaɗen karatu a wannan yanayi na matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Uba Sani ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa, na ganin ta samar da ilimi kyauta a matakan Firamare da Sakandare ga ɗaukacin ɗaliban jihar Kaduna.

Makarantun da Uba Sani ya ragewa kudin karatu

Makarantun da Uba Sani ya sanar da rage kuɗaɗen na su akwai Jami'ar jihar Kaduna (KASU), Kwalejin aikin lafiya na Shehu Idris da ke Makarfi, Makarantar koyon aikin jinya ta jihar Kaduna da aka rage yawan kuɗaɗensu da kaso 30%.

Haka nan kuma Gwamna Uba Sani ya sanar da rage kaso 50% na kuɗaɗen a makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic da kuma kwalejin ilimi na Gidan Waya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwar da cire tallafin man fetur ya jefa su a ciki.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Gwamnan APC Na Arewa Zai Ɗauki Matasa 7,000 Aiki Na Musamman a Jiharsa

Zai rage yawan ɗaliban da ke barin makaranta

A zantawarsa da Legit.ng, Dakta Alamuna Nuha, shugaban riƙo na sashen nazarin harsunan Najeriya na Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), ya yi tsokaci gameda wannan mataki da Gwamna Uba Sani ya ɗauka.

Ya ce wannan wani ɓangare ne na alƙawuran da gwamnan ya ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe, wanda kuma ya samu ikon cikawa a yanzu.

Ya yabawa Uba Sani bisa ƙoƙarin rage kuɗin makarantar da ya yi, inda ya ce hakan zai taimaka sosai wajen rage yawan ɗaliban da ke barin makaranta saboda rashin kuɗi.

Ya ce a baya ɗalibai da dama sun bar karatu sakamakon matsin tattalin arziƙin da aka shiga, ta yadda wasu ke gwammacewa su yi sana'a da kuɗaɗen da ke hannayensu maimakon zuwa makaranta.

Uba Sani ya soki rabon tallafin 8,000 na Tinubu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin da gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya yi dangane da rabon tallafin naira 8,000 da gwamnatin Tinubu ta so ta yi a baya.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Ministocin Tinubu Da Ke Karbar Fansho a Jihohinsu Da Dalilin Hakan

Gwamnan ya ce hakan ba komai ba ne face yaudara, kuma ya koka kan yadda aka tsame mutanen karkara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng