Gwamnatin Tinubu Za Ta Kashe Biliyan 1.37 Kan Wajen Kwanan Ministoci 45
- Zababbun ministocin shugaban kasa Bola Tinubu za su dunga samun miliyan 343.25 duk wata na kudin gida
- Hakan ya kasance ne bisa ga bayanan da aka wallafa a shafin yanar gizo na hukumar tattara kudaden shiga
- Baya ga kudin gida, sauran alawus da ministocin za su amfana da shi sun hada da na masu hidimar gida, kudin kayan amfani da na kayan alatu
Jaridar Punch ta rahoto cewa alawus din gidajen sabbin ministoci da aka nada na iya kaiwa naira miliyan 343.25 duk shekara.
Da wannan kudade da za a ware masu duk shekara, gwamnatin tarayya za ta kashe naira biliyan 1.37 kan wajen kwanan zababbun ministoci 45 cikin shekaru hudu.
Wannan alawus din ya kasance bisa bayanan da aka tattara daga wata takarda da aka samu a shafin yanar gizo na hukumar tattara kudaden shiga.
Jerin alawus da ministocin Tinubu za su amfana da shi
- Wannan ya kunshi alawus din kudin gida (kaso 200 na ainahin albashi)
- Ma'aikatan gida (kaso 75 na ainahin albashi)
- Kayan amfanin gida (kaso 30 na ainahin albashi)
- Kayan daki (kaso 300 na ainahin albashi)
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kuma, yayin da za a dunga biyan alawus din duk wata, za a biya na kayan gida sau daya ne a shekaru hudu.
Shugaban kasa Tinubu ya rabawa ministoci aiki
Ku tuna cewa a kwanan ne shugaban kasar ya sanar da aikin da ya bai wa kowanne daga cikin ministocinsa.
An tattaro cewa babu mutane uku da shugaban kasar ya zaba cikin wadanda za su amfana daga alawus din gidan.
Mutanen da abun ya shafa sune Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna; Stella Okotete, tsohuwar shugabar matan All Progressives Congress (APC) na kasa da Danladi Abubakar, zababben minista daga jihar Taraba.
Dalilin da yasa majalisar dattawa bata tabbatar da ministocin Tinubu uku ba
Da farko, majalisar dattawa ta ki tabbatar da zababbun ministocin shugaban kasa Tinubu uku, inda ta bayyana dalili na tsaro a matsayin hujja.
Hukuncin ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu ruwa da tsaki a siyasar kasar, musamman ma na El-Rufai, wanda aka tun farko ya nuna ya fi son tafiya karo karatunsa fiye da zama minista.
Daga cikin wadanda aka tantance da tabbatar da su akwai Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas wanda yake ministan babban birnin tarayya a yanzu da Wale Edun, ministan kudi.
‘Ya ‘yan fitattun siyasa 12 da ke fantamawa a gwamnati
A wani labari, ba bakon lamari ba ne a ga yaro ko ‘danuwan ‘dan siyasa ya shiga harkar tafiyar da shugabanci, an saba ganin hakan a fadin Duniya.
A wani dogon rahoto da Daily Trust ta fitar, ta tattaro wasu ‘ya ‘ya da su ka yi amfani da dama da sunan gidajensu, su ka shiga siyasa a kasar nan.
Asali: Legit.ng