Ministan Matasa Mai Shekara 60, Akanta a Tsaro da Abubuwan Mamaki a Ministoci

Ministan Matasa Mai Shekara 60, Akanta a Tsaro da Abubuwan Mamaki a Ministoci

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya kafa gwamnatinsa, a makon mai zuwa zai rantsar da wadanda za su zama ministocin tarayya.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu abubuwa da su ka ba mutane mamaki wajen rabon kujerun:

Gwamna Ministoci
Bola Tinubu zai rantsar da Ministovi Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

1. Badaru da Bello Matawalle a Ministoci

Kusan babu abin da ake magana kamar yadda tsofaffin Gwamnonin jihohi, Muhammad Badaru da Bello Matawalle za su jagoranci ma’aikatar tsaro.

Badaru ‘dan kasuwa ne wanda ya karanta ilmin akawu, shi ma mataimakinsa, Bello Matawalle bai da wata kwarewa ko sanin kan aikin abin da ya shafi tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Ministan ‘yan sanda babu lafiya

Majiyoyi da yawa sun shaidawa Legit.ng Hausa Ibrahim Geidam mai shekara 66 da zai zama ministan ‘yan sanda bai da lafiya, ta kai ya na yawo da sanda.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Tinubu Ya Yi Koyi da Buhari, Ya Rike, Ya Hana Kowa Ministan Fetur

Tun farko an yi mamakin ganin yadda Sanatan mai-ci ya shiga jerin ministocin kasar.

3. Dele Alake zai zama Ministan ma’adanai

Shugaban kasa ya bada kafa wajen nada Dele Alake a ministan ma’adanai. Mutane duk sun rinjaya ‘dan siyasar ne zai zama Ministan yada labarai na kasa.

Yanzu Alake ya na ba shugaban kasa shawara a kan labarai, dabaru da hakoki na musamman.

4. Festus Keyamo: Ministan jirgi bai san jirgi ba

An yi tunanin wanda ya san kan harkar ne zai zama ministan jiragen sama. Ko da yake kafin shi, Lauyoyi irinsu Femi Fani Kayode sun taba rike wannan kujera

5. Nyesom Wike: ‘Dan PDP ya zama Ministan APC

An shafe shekaru ‘Yan Arewa na zama ministocin birnin tarayya, gwamnatin Tinubu ta bada mamaki da ta dauko Nyesom Wike, za ta ba shi wannan aiki.

6. Dattijon Ministan Matasa

Abubakar Momoh wanda za a rantsar a Ministan matasa ba matashin ba ne. tun 1988 Momoh ya fara koyawar a jami’a, ana zargin ‘dan siyasan ya kai shekara 60.

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Zunubai 10 da Hukumar DSS Ta Yi Amfani Da Su A Kan Nasir El-Rufai

7. Babu Minista daga Kaduna

A jerin da aka fitar, an ji Adebayo Adelabu aka zaba ya rike ma’aikatar makamashi, kujerar da masu fashin baki su ka ce an warewa tsohon Nasir El-Rufai ne.

Jihar Kaduna ba ta da wakilci a majalisar FEC wanda hakan zai iya saba doka.

Tinubu ya rike kujera 1

Kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi a lokacin da ya ke ofis na tsawon shekaru takwas, kun ji labari Bola Ahmed Tinubu bai bada ministan fetur ba.

Sabuwar gwamnati ta barka ma'aikatar man fetur, yanzu an samu ministan gas. Ekerikpe Ekpo wanda ta fito daga Akwa Ibom ta na cikin ministocinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng