Abba vs Gawuna: Jigon APC Yana Barar Addu'a Daga Yan Najeriya Don APC Ta Yi Nasara
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya roki yan Najeriya da su taya APC da addu'a don ta yi nasara a shari'ar Nasir Gawuna da Abba Gida-gida
- Sanata Barau Jibrin ya nuna karfin gwiwar cewa APC za ta dawo da karfinta a jihar Kano
- Sai dai ya ce za a cimma haka ne idan shugabannin jam'iyyar a Kano suka hada kansu sannan suka dukufa wajen addu'a
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya roki yan Najeriya musamman mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), da su taya jam'iyyar da addu'a don ta yi nasara a kotun zabe.
Sanata Jibrin mai wakiltan Kano ta arewa ya nuna yakinin cewa APC za ta dawo da karfinta a jihar Kano, yana mai rokon masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar da su hada kansu, rahoton Vanguard.
Mu dage da addu'a komai a hannun Allah yake, Barau
Da yake magana a ranar Talata, a majalisar dokokin tarayya a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin mataimakan shugaban kananan hukumomi a karkashin inuwar ALGOVC, reshen jihar Kano, Sanata Barau ya bayyana cewar da addu'o'i da hadin kai, APC za ta yi nasara a kotu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
APC na kalubalantar ayyana Abba Yusuf na NNPP da aka yi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a jihar Kano a ranar 18 ga watan Maris a kotun zabe.
Barau ya ce:
"Muna addu'a sannan muna fatan cewa sakamakon kotun zaben zai kawo nasara garemu. Komai a hannun Allah yake. Mu hada kanmu sannan mu yi aiki tare. Da izinin Allah, komai lokaci ne, za mu dawo da karfinmu a jihar Kano.
"Kamar yadda yake a yanzu, muna cikin masu adawa kuma saboda haka akwai abubuwa da dama da ake tsammani daga garemu. Ya kamata mu hada kai sannan mu yi aiki tare don ra'ayin jam'iyyarmu."
Da yake yaa ma mataimakan shugabannin kananan hukumomin kan ziyararsu, Sanata Barau wanda ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki tare da su don inganta rayuwar talakawa ya ce:
"Kananan hukumomi na da matukar muhimmanci. Za mu ci gaba da aiki tare da ku don magance matsalolin da mutanenmu ke fuskanta. Muna alfahari da ku. Mu ci gaba da aiki tare."
Rahoton ya kawo cewa da farko shugaban kungiyar, Alhaji Yakubu Musa Naira, ya ce sun zo majalisar dokoki ne don taya Sanata Barau murnar zabarsa a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa da aka yi.
Ganduje ya magantu bayan ganawa da Wike
A wani labarin, mun ji cewa jawabin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje na baya-bayan nan ya kara karfafa rade-radin da ake yi na zargin sauya shekar tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Wannan ya kasance ne yayin da Ganduje ya bugi kirgin cewa jam'iyyar za ta kara karfi, cewa ana kan tattaunawa domin samun wasu jam'iyyun adawa da za su yi maja a APC.
Asali: Legit.ng