Adeyanju Deji Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Atiku Ya Ziyarci Rabiu Musa Kwankwaso

Adeyanju Deji Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Atiku Ya Ziyarci Rabiu Musa Kwankwaso

  • Mai sharhi a kan al'amuran siyasa, Adeyanju Deji, ya yi magana kan ziyarar da Atiku ya kai wa Kwankwaso a gidansa
  • Ya ce Atiku ya ziyarci Kwankwaso ne saboda an faɗa ma sa cewa kotu za ta ce a sake zaɓe tsakaninsa da Tinubu
  • Adeyanju ya ce an yaudari Atiku da cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe za ta ce a zo a sake gudanar da zaɓen

FCT, Abuja - Fitaccen mai sharhi kan al'amuran siyasa, Adeyanju Deji, ya bayyana dalilin ziyarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai wa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana batun zaiyarar da Atiku ya kai ma sa a shafinsa na Facebook.

An bayyana dalilin zuwan Atiku wajen Kwankwaso
Adeyanju Deji ya fadi dalilin ziyarar da Atiku ya kai wa Kwankwaso. Hoto: @KwankwasoRM, @Adeyanjudeji
Asali: UGC

Atiku na tsammanin za a sake zaɓe tsakaninsa da Tinubu

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Aje Mataimakinsa a Gefe Guda, Ya Zabo Mace a Matsayin Abokiyar Takararsa Kan Dalili 1 Rak

Adeyanju ya ce Atiku ya ziyarci Kwankwaso ne saboda an faɗa ma sa cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe za ta ba da umarnin sake gwabzawa tsananinsa da Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adeyanju ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter @adeyanjudeji, a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta.

A kalaman Adeyanju:

“Ziyarar da Atiku ya kai wa Kwankwaso ya yi ta ne saboda wasu mutane sun yaudaresa da cewa kotun zaɓe za ta ba da umarnin a sake zaɓe tsakaninsa da Tinubu.”

Shehu ya fadi abinda Atiku da Obi za su yi bayan yaken hukunci

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan kan tsokacin da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi dangane da shari'ar da Atiku da Peter Obi ke yi da Tinubu.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Ya Bayyana Hanya 1 Da Za a Iya Tsige Shugaba Tinubu

Shehu Sani ya bayyana cewa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour, za su karɓi kowane irin hukunci ne kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yanke kan shari'arsu da Tinubu.

Atiku da Obi dai na ƙalubalantar zaɓen 2023 da Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC ya lashe a gaban kotun.

Adeyanju ya faɗi hasashensa kan shari'ar su Atiku da Tinubu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan hasashen da fitaccen mai sharhi kan al'amuran siyasa Adeyanju Deji ya yi kan sakamakon shari'ar da Atiku Abubakar da Peter Obi ke yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Adeyanju ya ce hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe za ta yanke ba zai yi wa Atiku Abubakar da Peter Obi daɗi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng