Tsofaffin Kwamishinoni Sun Lallaba, An Roki Tinubu ya Ba El-Rufai Minista a Gwamnati

Tsofaffin Kwamishinoni Sun Lallaba, An Roki Tinubu ya Ba El-Rufai Minista a Gwamnati

  • Wasu da ke tare da Nasir El-Rufai sun tunawa Bola Ahmed Tinubu abin da ya faru a zaben bana
  • Tsofaffin Kwamishonin Kaduna sun ce mai gidansu ya cancanci zama Minista a gwamnatin nan
  • ‘Yan kungiyar Like Minds Forum of Nigeria sun zargi wasu da idonsu ya rufe da bata El-Rufai

Kaduna - Kwamishonin da su ka yi aiki da Nasir El-Rufai a jihar Kaduna, sun roki Bola Ahmed Tinubu ya ba mai gidansu mukami a gwamnatinsa.

A rahoton da mu ka samu daga Daily Trust, an fahimci tsofaffin kwamishinonin sun roki shugaban Najeriyan ka da ya janye alkawarin da ya dauka.

Kamar yadda tsofaffin jami’an gwamnatin su ka shaida a karkashin inuwar Like Minds Forum of Nigeria, El-Rufai mutumin shugaban Najeriya ne.

Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai ya goyi bayan Bola Tinubu Hoto: @bashirelrufai
Asali: Twitter

Kungiyar magoya bayan El-Rufai

Kara karanta wannan

Za ayi kuskure: Ƙusa a APC Ya Gargaɗi Tinubu a Kan Watsi da El-Rufai Wajen Naɗa Ministoci

Kwamishinonin bayan sun hadu ne a garin Kaduna, su ka ce har wadanda su ke abokan fadan Malam El-Rufai, sun san alakarsa da shugaban kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dr. Shehu Usman Muhammad shi ne yake jagorantar Like Minds Forum of Nigeria tare da sauran kwamishinonin da ya yi aiki tare da su a jihar Kaduna.

Ragowar ‘yan kungiyar sun hada da Hafsat Baba wanda ta rike kwamishinar kula da al’umma da Ibrahim Hussaini wanda ya yi kwamishinan muhalli.

A tafiyar akwai tsohuwar kwamishinar kiwon lafiya, Dr. Amina Mohammed Baloni. Maganar da ake yi tsohon Ministan Abujan ya na kasar waje yanzu.

El-Rufai ya taimaki Tinubu a 2023

A cewar wadannan mutane, tsohon mai gidansu ya taka rawar gani a zaben shugabancin kasa, ya goyi bayan mulki ya koma yankin kudu.

Jaridar ta rahoto kungiyar ta na cewa zargin da ake yi wa tsohon gwamnan Kaduna, yunkuri ne kurum na masu neman bata masa suna ba komai ba.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: An yi auren babban dan El-Rufai amma bai halarta ba, bayanai sun fito

‘Yan kungiyar sun tunawa Bola Ahmed Tinubu cewa El-Rufai ya hidimtawa kasarsa, ya kawo gyare-gyare, kuma har yanzu bai gaji da yin bauta ba.

Like Minds Forum of Nigeria ta ce mutanen Kaduna, Arewacin Najeriya da daukacin kasar nan su na bakin cikin da aka gaza tantance ‘dan siyasar.

Kuskure ne ayi watsi da El-Rufai

Rahoto ya zo a baya cewa hugaban hukumar VON, Cif Osita Okechukwu ya na ganin kuskure ne Bola Ahmed Tinubu ya hana Nasir El-Rufai mukami.

Idan tsohon Gwamnan na Kaduna ya zama minista, 'dan siyasar ya na ganin APC za ta amfana a zaben 2027 domin El-Rufai zai yi aikin da za a yaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng