Ganduje: Abin da Ke Jawo Mataimakan Gwamnonin Jihohi Su Yi Fada da Gwamnoni
- Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin tsofaffin Gwamnonin jihohi a sakatariyar jam’iyyar APC
- Shugaban APC ya yi magana game da alakar Gwamnonin da Mataimakansa da abin ke jawo rigingumu
- Ganduje wanda ya san gwamnati da kyau, ya ce dokar kasa ba ta yankewa Mataimaki wani aiki ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana game da alakar gwamnonin jihohi da mataimakin gwamnonin jihohi.
The Guardian ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya hadu da tsofaffin Gwamnonin jihohi, ya fadi abin da ke jawo rikici a gidajen gwamnatoci.
Shugaban jam’iyyar APC na kasan ya zargi ‘yan kanzagi da hura wutar rikicin siyasar da ake samu, yanzu haka gwamnatin NNPP ta na bincikensa a Kano.
Mataimakan gwamnoni ba banza ba
‘Dan siyasar ya ke cewa bai kamata a rika raina mataimakan gwamnoni ba domin amfaninsu ya na tashi a duk lokacin da gwamna ya shiga wata larura.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tun da kundin tsarin mulkin kasa bai yi bayanin nauyin da ke kan wuyan mataimaki ba, shi kan shi Ganduje ya misalta su da tayar faci a mota.
Ko da direba bai bukatar tayan a lokacin da abubuwa su ke tafiya kalau a mota, ya ce da zarar ya shiga matsala zai fara neman inda karamar tayar ta shiga.
Dr. Ganduje ya rubuta littafi
Ko a yanzu haka ana samun matsala tsakanin wani gwamna da mataimakin shi, saboda shawo kan irin haka ‘dan siyasar ya rubuta littafi a kan batun.
P/Times ta ce tsohon Gwamnan na jihar Kano ya rubuta littafi mai suna “Deputising and Governance in Nigeria” da ya shafi mulki da taimakawa masu iko.
"Idan ka na mataimaki, sai ka tsaya gefen gwamna domin ka saurare shi da kyau kuma shi ma ya saurare ka, za a ce ai shirme kurum ka ke fada.
Idan ka shiga gaba domin bada kariya ko da an samu hadari ko miyagun abubuwa kamar macizai su fado, ‘yan kanzagi za su ce ka sha gaban shi.
Idan ka girmama mai gidanka, ka tsaya a bayan shi, ‘yan kanzagi za su ce ka na sanya, ka yi watsi da shi, to yanzu wani matsayi za ka dauka?"
- Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje a gidan gwamnatin Kano
Ganduje wanda ya yi aiki da Rabiu Musa Kwankwaso na tsawon shekaru takwas, ya ce bai bari irin wadannan mutane sun hada shi fada a mulki ba.
Har Rabiu Kwankwaso ya kammala mulki, ya mikawa Ganduje ba a taba jin wani sabani a tsakaninsu ba, duk da dai Hafizu Abubakar ya bar shi.
A 2018 Farfesa Hafiz Abubakar lokacin ya na Mataimakin gwamnan jihar Kano ya ce Ganduje ya na azabtar da shi, daga baya ya sauka daga kujerarsa.
Asali: Legit.ng