Naɗa Ministoci: 'Dan APC Ya Gargaɗi Bola Tinubu a Kan Watsi da Nasir El-Rufai

Naɗa Ministoci: 'Dan APC Ya Gargaɗi Bola Tinubu a Kan Watsi da Nasir El-Rufai

  • Osita Okechukwu ya na ganin kuskure ne Bola Ahmed Tinubu ya bar Nasir El-Rufai ya tafi a banza
  • Idan tsohon Gwamnan ya zama minista, jagoran na APC ya na ganin APC za ta amfana a zaben 2027
  • Cif Okechukwu ya na da ra’ayin cewa El-Rufai ya cancanta ya kula da bangaren makamashi a Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Osita Okechukwu wanda ya na cikin wadanda aka kafa jam’iyyar APC da su a Najeriya, ya yi kira da babbar murya ga Bola Ahmed Tinubu.

Osita Okechukwu ya gargadi Mai girma Bola Ahmed Tinubu cewa ka da ya cire Mallam Nasir El-Rufai a ministocinsa, Punch ta kawo rahoton.

An aika sunan Nasir El-Rufai zuwa majalisa, kuma har tsohon gwamnan ya bayyana a gaban Sanatoci, daga baya aka ji cewa ba a amince da shi ba.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: An yi auren babban dan El-Rufai amma bai halarta ba, bayanai sun fito

Nasir El-Rufai
El-Rufai, Tinubu da Buhari Hoto: @officialabat
Asali: Twitter

Rashin El-Rufai babbar asara ce

Da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja a ranar Lahadi, Darekta Janar na hukumar VON ya kuskure ne a ajiye tsohon Gwamnan Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okechukwu ya na da ra’ayin cewa El-Rufai zai bada gagarumar gudumuwa a gwamnati musamman idan ya samu mukami a bangaren wuta.

"Buhari ya yi asarar rasa El-Rufai, kuma babu wanda zai so kasarmu ko Shugaban kasa Tinubu ya rasa wannan ‘dan baiwa.
Jam’iyyarmu ta APC za ta amfana sosai da ministocin da su ka yi aiki a lokacin da mu ka dumfari babban zaben Najeriya a 2027.
Korar shi daga gwamnatin tarayya zai yi sanadiyyar fatattakar wasu karin ‘Yan Najeriya daga bangaren wutar lantarki.
Mutanen Najeriya da-dama su na kyale wutar gwamnati da ake fama da matsaloli yayin da talakawan kasar ke kukan tsada.
Mu na bukatar mutum na dabam kamar Nasir El-Rufai ya shawo kan matsalar lantarki."

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Zunubai 10 da Hukumar DSS Ta Yi Amfani Da Su A Kan Nasir El-Rufai

- Osita Okechukwu

Gaskiyar magana a kan El-Rufai

Kamar yadda Daily Post ta rahoto, shugaban na VON ya ce bai cikin ‘yan kanzagin Nasir El-Rufai, kuma bai tunanin bai da tamka a gwamnatin Najeriya.

Illa iyaka ya na ganin tsohon Ministan na birnin Abuja ya fi sauran ire-irensa da-dama sanin yadda za a kawo gyara, musamman a bangaren makamashi.

Ya aka yi aka cire El-Rufai?

Kun samu rahoton da ya nuna da kamar wahala Nasir El-Rufai, Abubakar Sani Danladi da Stella Okotete su iya zama Ministoci a gwamnati mai-ci.

Abin da ya faru da mabiyan El-Zakzaky sun taimaka wajen yakar tsohon Gwamnan Kaduna baya ga tulin korafi da kara a kotu da zargi da ke kan El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng