Abokin Tafiyar Buhari Ya Yi Kaca-Kaca Da Tinubu a Kan Tallafin Fetur Da Emefiele
- Tunde Bakare ya yi jawabin da ya ba shi damar tofa albarkacin bakinsa a kan gwamnatin tarayya
- Faston na Citadel Global Community ya bukaci a cafko wadanda su ka saci kudin tallafin man fetur
- Bakare ya na so Bola Tinubu ya yi gaskiya wajen binciken duk mutanen da ake zargi sun aikata laifi
Lagos - Tunde Bakare wanda ‘dan siyasa ne kuma malamin addinin kirista, ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya ga bayan duk barayin kasar nan.
The Cable ta ce Fasto Bakare a wata huduba da ya gabatar a ranar Lahadi, ya ja kunnen shugaban kasa ya hukunta wadanda su ka cuci al’umma.
Limamin cocin Citadel Global Community wanda aka fi sani da Latter Rain Assembly a baya, ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a APC a zaben 2023.
Bakare ya bayyana cewa bai adawa da janye tsarin tallafin fetur da aka yi, amma ya na ganin ya kamata a yaki rashin gaskiyar da aka yi ta tafkawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kashe barna ba mutane ba
Yayin da ya gamsu tashin farashin man fetur ya na wahalar da al’umma, ya kuma bukaci gwamnati ta yaki tsarin ne ba ta ga bayan ‘yan Najeriya ba.
Faston yake cewa shugaba Tinubu ya yi jawabin da ya tabbatarwa jama’a an tara Naira tiriliyan 1 da gwamnati ta daina biyan tallafin man fetur.
Idan da gaske Tinubu ya na tare da talakawa, faston ya ce dole a fito a fallasa ‘yan kasuwar da su ka rika cin kudi da sunan za a samu saukin fetur.
Jawabin Tunde Bakare
Su wanene ‘yan fasa kauri da barayin da su ka rika damfarar kasarmu da sunan tallafin fetur? Su wanene mutanen da ba su da suna?
Mai girma shugaban kasar Najeriya idan da gaske ka na bangaren talakawa ne, to ka kashe rashin gaskiya ne ba mutanen Najeriya ba."
- Tunde Bakare
A jawabin da ya yi a cocinsa da ke Ikeja a Legas, Vanguard ta ce Bakare ya soki gwamnatin Bola Tinubu a kan yunkurin yaki da kasar Nijar.
Da yake maganar binciken CBN da EFCC, limamin ya zargi gwamnati da bita da kulli, ya kuma ce zaben 2023 ya nuna dole sai APC ta sake yin shiri.
Za a tsinci fetur a N720
Farashin fetur zai kuma lulawa inda aka ji dillalai sun nuna shigo da fetur ya zama aiki, wasu sun fara hakura saboda irin tashin da Dala ta ke yi.
Daga kusan N200 da Bola Tinubu ya gaji farashin fetur a hannun Muhammadu Buhari, ya harba farashin lita zuwa N620 tun a kwanakin farko.
Asali: Legit.ng