Shugaban kasa: Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son gaje Buhari a 2023

Shugaban kasa: Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son gaje Buhari a 2023

  • Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son shiga tseren kujerar shugaban kasa a babban zaben 2023
  • Bakare ya bayyana kudirin nasa ne a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, tare da ajandarsa na son daidaita kasar
  • Malamin addinin ya kasance tsohon abokin takarar shugaba Buhari a zaben 2011 karkashin jam’iyyar CPC

Babban faston Najeriya kuma limamin cocin Citadel Global Community Church, Tunde Bakare, ya ayyana aniyarsa ta son takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

A wani jawabi da ya yi a wani taron yanar gizo a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, Bakare ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta don jagorantar kasar daga shekarar 2023, Channels tv ta rahoto.

Shugaban kasa: Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son gaje Buhari a 2023
Shugaban kasa: Fasto Tunde Bakare ya ayyana aniyarsa ta son gaje Buhari a 2023 Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Ya ce:

“Dangane da koma bayan da kasar ke ciki, muna bukatar shugaba wanda zai iya daidaita kazamin bambance-bambancen da ake fama da shi a yanzu, ya maido da kyakkyawar alakar da ke tsakanin al’umman kasar tare da inganta tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Daga Ƙarshe, Ministan Buhari ya ayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan ne ya kawo ni cikin tafiyar PTB. A takaice PTB ce alamar Fasto ‘Tunde Bakare a yanzu. PTB ita ce ajandar aiki ta 16."

Babban limamin cocin ya ce ba wai don muradin kansa bane yake son zama shugaban kasa illa don burinsa na sabonta Najeriya wanda yake kulle da shi a zuciya tun daga lokacin kuruciya.

Ya kuma jadadda cewa bisa gaskiya yake son hidimtawa kasar a matsayin shugaban kasar Najeriya na goma sha shida.

Malamin addinin ya yi gargadin cewa gabannin babban zaben na 2023, an sanya kudu yin gaba da arewa, yayin da aka sa kiristoci adawa da musulmai., rahoton Vanguard.

Bakare ya kasance abokin takarar Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ya yi takarar shugaban kasa a shekarar 2011 karkashin jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC).

Kara karanta wannan

Karfin hali: Mace ta farko a APC ta ayyana aniyar gaje kujerar Buhari a zaben 2023

2023: Jerin jihohi 8 da PDP ka iya shan kaye idan har ta baiwa dan arewa tikitin shugaban kasa

A wani labari na daban, gabannin babban zaben 2023, ana ta rade-radin cewa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta baiwa dukkanin yankunan kasar damar shiga tseren neman tikitinta na shugaban kasa.

Sai dai kuma, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue wanda shine shugaban kwamitin tsarin karba-karba na PDP ya yi watsi da ikirarin da wasu majiyoyi suka yi.

Ya ce kwamitin karba-karban ya yanke hukunci kan lamarin amma kwamitin NEC bai riga ya tabbatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel