Yadda Masu Rike da Madafan Iko Su ka yi wa El-Rufai Taron Dangi a Nadin Ministoci
- Da farko Nasir El-Rufai ya nuna bai sha’awar sake rike wani mukami, kafin a iya shawo kan shi
- Bayan an lallabi tsohon Gwamnan na Kaduna, ya ba Bola Tinubu shawarar yadda za a gyara wuta
- Kwatsam sai aka ji duk da ya bayyana a gaban majalisa, jami’an tsaro sun dakatar da sunan El-Rufai
Abuja - Tun kafin Shugaban kasa ya janye sunansa ko ya sake maidawa a cikin ministoci, sai aka ji Nasir El-Rufai ya tattara ya bar Najeriya.
Daily Trust ta ce an yi tunanin Nasir El-Rufai zai zama Ministan lantarki da makamashi a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, sai lamari ya canza.
Tun a ranar Juma’a, jagoran na jam’iyyar APC ma-ci ya bar Najeriya zuwa Masar, ya kuma nunawa shugaban kasa bai sha’awar ya rike mukami.
Lamarin tsaro ko tsoron 2027 da 2031
Kafin ya bar kasar, rahoton ya ce sai da El-Rufai ya zauna da masu ruwa da tsaki a kan harkar wuta, ya roki su goyi bayan wanda zai zama minista.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bincike ya nuna cewa rikicin siyasa ne da sabaninsa da wasu har a fadar shugaban kasa ya jawo aka dakatar da Malam El-Rufai daga rike mukami.
"Da alama wasu mutane da su ke da karfi a Najeriya ba su natsu da gyare-gyaren da El-Rufai zai kawo a bangaren lantarki da makamashi ba.
- Majiya
Majiyar ta ce a lokacin ya na ministan birnin tarayya a zamanin Olusegun Obasanjo, an yi yunkurin a kai shi kasa saboda gyare-gyaren da ya fito da su.
Tun kafin tsohon Gwamnan na Kaduna ya zauna da shugaba Bola Tinubu, rahoton ya ce ya yanke shawarar watsi da tayin mukami a gwamnatin tarayya.
Idan har DSS za ta yarda da wadanda ake zargi da laifin rashin gaskiya, na-kusa da ‘dan siyasar su na ganin makirci ne kurum ya jawo aka kunyata shi.
Punch ta ce tun lokacin kamfe, Gwamnan ya fadawa ‘dan takaran APC (a lokacin), zai fi so ya koma kasar waje, bai harin rike wata kujera a gwamnatinsa.
Fadar El-Rufai a wajen Tinubu
Da aka shawo kan shi ne sai ya hada shugaban kasa da kwararru a harkar mai da lantarki irinsu Jimi Lawal; Olu Verheijen; Eyo Ekpo da Tolu Oyekan.
Ana haka kuma sai wasu da ke rike da madafan iko a sabuwar gwamnati su ka fara shakkar jawo tsohon Ministan, su na ganin zai zama barazana a zabe.
Malam ne ya kawo yadda za a gyara wuta da mai kuma Tinubu ya yi na'am, a lokacin da aka samu cikas, bai samu goyon bayan shugaban kasar sosai ba.
DSS ta fitar da rahoto mara kyau
Daga nan sai aka ji wani Aminu Yusuf ya aikowa Hadimin shugaban kasa takarda a madain DSS, ya na bada shawarar dakatar da nada El-Rufai a minista.
Hukumar ta rubuta wasika a ranar 4 ga Agusta, ta na jero laifuffukan da ke wuyan tsohon Gwamnan tare da Abubakar Sani Danladi da Stella Okotete.
Malam El-Rufai bai sa a kai ba
Dama tun can kun samu rahoto tsohon Gwamnan ya nuna rokon shi Bola Tinubu ya yi domin su yi aiki tare, bai kwallafa rai da mukami a shekarunsa ba.
Rahoton DSS ya jawo sha’awar sake zama Minista ya fita daga ran Malam Nasir El-Rufai, ya bada shawarar a maye gurbin shi da wani a jerin Ministoci.
Asali: Legit.ng