El-Rufai Ya Daina Sha’awar Zama Ministan Tinubu, Ya Bada Sunan Sabon Madadinsa
- Watakila Nasir El-Rufai ba zai shiga cikin ministocin da Bola Tinubu zai yi aiki da su a mulki ba
- A wani zama da tsohon Gwamnan ya yi da shugaban kasa, ya nuna ya daina sha’awar mukami
- Hakan ya biyo bayan cikas da El-Rufai ya samu daga jami’an tsaro wajen tantance shi a Majalisa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, ya bayyana cewa Nasir El-Rufai bai sha’awar zama minista a sabuwar gwamnatin tarayya.
Nasir El-Rufai bai sha’awar yin aiki da Bola Ahmed Tinubu bayan abin da ya faru a wajen tantance wadanda ake so su zama ministoci a kasar nan.
Da aka yi zama da tsohon gwamnan na jihar Kaduna a makon nan, wasu majiyoyi sun shaida cewa ya fadawa Bola Tinubu bai sha’awar rike mukami.
Malam El-Rufai ba zai shiga gwamnati ba?
Malam Nasir El-Rufai ya nuna zai bada gudumuwarsa wajen gyara kasa a matsayin mai zaman kan shi, ba tare da ya taka rawar gani a gwamnati ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon ministan ya nunawa shugaba Bola Tinubu cewa ya na bukatar lokaci domin ya maida hankali a kan karatun digir-digir da yake yi a kasar waje.
El-Rufai ya na kokarin kammala digirinsa na PhD a wata jami’a da ke kasar Netherlands a Turai.
Wanda zai canji El-Rufai
Rahoton ya ce idan ana bukatar shawararsa a kan wanda zai iya rike kujerar minista a gwamnatin tarayya, El-Rufai ya bada sunan Jafaru Ibrahim Sani.
Malam Jafaru Ibrahim Sani ya rike matsayin kwamishina a ma’aikatar kananan hukumomi, ilmi da muhalli a lokacin ‘dan siyasar ya na Gwamna.
Idan an gagara shawo kan shi, watakila a dauki Jafaru Sani ko wani dabam daga Kaduna domin a samu wanda zai wakilci jihar a majalisar ministoci.
Haduwar El-Rufai da Tinubu
Da jin labarin jami’an tsaro ba su kai ga yin na’am da nadin shi a matsayin minista ba, El-Rufai ya na dawowa, ya nemi ya zauna da shugaban Najeriya.
A lokacin da labarin ya fito, rahoton ya ce Malam ya iso Najeriya daga Landan kenan.
A wajen zaman ne Bola Tinubu ya fada masa SSS ta aiko korafi game da shi, kuma ana bukatar a duba rahoton, a nan ya nuna bai bukatar wani mukami.
Yadda Tinubu ya nemi alfarmar El-Rufai
Kwanaki kun ji labari an gano bidiyo a Twitter inda Bola Tinubu da kan shi ya ke rokon Nasir El-Rufai ya yi aiki da gwamnatinsa idan an ci zabe.
A lokacin kamfe, Malam El-Rufai ya nuna cewa shekaru sun ci masa, saboda haka bai bukatar ya rike kujerar da ya bari tun a Mayun shekarar 2007.
Asali: Legit.ng