Duka Sanatocin Kudu Sun Huro Wuta, Sun Ce Dole Bola Tinubu Ya Kara Masu Ministoci
- Sanatocin yankin Kudu maso gabas sun yi tarayya a kan bukatar karin kujerun Ministoci a Najeriya
- A wani zaman majalisa da aka yi kafin a tafi hutu, Sanata Tony Nwoye ya bijiro da batun mukamai
- ‘Dan majalisar da sauran takwarorinsa sun ce kyau Bola Tinubu ya ware masu karin Ministoci biyu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Sanatocin Kudu maso gabas a majalisar dattawan Najeriya, sun bukaci karin kujerun Ministoci daga wajen Bola Ahmed Tinubu.
A rahoton ta da The Nation ta fitar, an ji cewa Sanatocin yankin na Kudu su na ganin cewa kyau a kara masu ministoci idan har za ayi adalci.
‘Yan majalisar su na so yankinsu su samu karin kujeru biyu a majalisar zartarwa ta kasa, su ka ce hakan zai sa su zama kusan daidai da kowa.
Tony Nwoye mai wakiltar Arewacin Anambra a majalisar dattawa ya kawo wannan magana a lokacin da majalisar ta zauna a makon nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ragowar Sanatoci 14 daga jihohin Kudu maso gabas sun yi tarayya da Sanatan LP a wannan kudiri yayin da ake korafin ana ware yankin.
Ministoci: An bar Kudu maso gabas a baya?
This Day ta ce Sanata Tony Nwoye ya na cewa yankinsa ne zai samu mafi karancin kujerun ministoci (biyar) a gwamnatin Bola Tinubu.
Wadanda aka zabo daga yankin su ne: Dr. Uju Kennedy Ohaneye (Anambra), Nkiru Onyejiocha (Abia) sai kuma Doris Uzoka-Anite (Imo).
Ragowar Ministoci daga jihohin su ne Uche Nnaji (Enugu) da Dave Umahi (Ebonyi),
Shi kan shi Sanata Dave Umahi wanda zai zama Ministan tarayya, ya na cikin Sanatocin da ke wakiltar yankin (mazabar Ebonyi ta Kudu).
Tinubu ya saba doka a rabon Ministoci
A cewar Nwoye, abin da Bola Tinubu ya yi, ya sabawa sashe na 5 (a) da (b) da kuma sashe na 4 (1) na dokar tsarin daidaito wajen rabo ta 2004.
Idan aka tafi a haka, Sanatan ya ce ba ayi adalcin da sashe na 14 (3) na kundin tsarin mulki ya bukata ba, majalisa ta yi alkawarin za a duba batun.
Za a binciki tsofaffin Ministoci?
Ku na da labari an karbi korafin kungiyar HEDA domin yin bincike a kan tsohon AGF, Abubakar Malami kuma an sanar da cewa ana daukar mataki.
Shugabannin hukumar ICPC sun ce sun karbi takardar korafin da aka aiko a kan Malami wanda ya na cikin masu kusanci da Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng