Abin Kirki Ya Yi Rana, Sanata Ya Kare Farfesa Wajen Tantance Ministoci a Majalisa

Abin Kirki Ya Yi Rana, Sanata Ya Kare Farfesa Wajen Tantance Ministoci a Majalisa

  • Farfesa Tahir Mamman ya na cikin jerin mutanen da Majalisa ta tantance domin zama Ministoci
  • Fitaccen Lauyan ya koyar da Kaka Shehu Lawan a lokacin da ya ke karantarwa a jami’ar UNIMAID
  • Sanatan bai manta alherin da Malaminsa ya yi masa ba, ya yi masa hallaci da ya zo Majalisar dattawa

Abuja - Tahir Mamman SAN ya ci karo da wani tsohon dalibinsa na jami’ar Maiduguri a lokacin da ya je majalisar tarayya domin tantance shi.

Farfesa Tahir Mamman SAN ya na cikin jerin mutanen da Bola Ahmed Tinubu ya bada sunayensu domin su zama ministoci a gwamnatin tarayya.

A wani bidiyo da ya shigo hannun Legit.ng Hausa, an ga yadda Sanata Kaka Shehu Lawan ya tsaya gaban abokan aikinsa, yana yabon Farfesan shi.

Tantance Ministoci a Majalisa
Sanatoci su na tantance Ministoci Hoto: The Senate President
Asali: Facebook

Tsohon dalibi ya yabi malaminsa

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Haduwa da Tinubu da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Kaka Shehu Lawan mai wakiltar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa ya bada labarin irin yadda Mamman ya kula da shi a lokacin ya na dalibi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanatan ya ce Farfesa Mamman ya kasance malaminsa kuma shugaban sashen kula da dalibai a lokacin da ya ke karatu a jami’ar nan ta UNIMAID.

Jawabin yabo daga Kaka Shehu Lawan

"Sunana Kaka Shehu Lawan, ina wakiltar mutanen kirkin Borno ta tsakiya, daga jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.
Wanda ya ke tsaye a gabanku shi ne Farfesa Tahir Mamman, ya taba zama malami na, shugaban sashe, shugaban tsangaya kuma shugaban bangaren dalibai
A lokacin da na ke aji biyu a jami’ar Maiduguri, ya koyar da ni ilmin shari’ar tsarin mulki, sannan a aji uku kuma, ya koyar da ni ilmin gudanar da shari’a.

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna Ya Jagoranci Jami’an Tsaro An Dura Gungun ‘Yan ta’adda Cikin Dare

Ina mai farin cikin sanar da ku cewa na kasance shugaban dalibai a lokacin ya na bangaren kula da dalibai. Kwamred Oshiomhole abin koyi na ne a lokacin."

- Kaka Shehu Lawan

Premium Times ta rahoto Sanatan na Borno ya na koro bayanin yadda Tahir Mamman ya taimaka masu ta fannin boko da kuma wajen samun daki.

Ko a lokacin da ba a ba dalibai daki a aji uku, Farfesa Mamman ya yi sanadiyyar da Kaka Lawan da abokan karatunsa su ka samu daki, kuma su ka wataya.

An ki amincewa da mutum 3 su zama Ministoci

Ku na da labari cewa Nasir El-Rufai (Kaduna), Stella Okotete (Delta) da Abubakar Danladi (Taraba) ba su san matsayarsu ba wajen zama Ministocin kasa.

Bayan shekaru 20, tarihi ya maimata kan shi, El-Rufai ya sake samun matsala wajen zama Ministan tarayya, a yanzu ana jiran rahoton jami'an tsaro a kan shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng