Minista: "Mai Tsattsauran Ra'ayi Ba Shi Da Wuri A Mukami", Shehu Sani Ya Yi Shagube Ga El-Rufai
- Sanata Shehu Sani ya ce daya daga cikin wadanda majalisa ta ki tabbatarwa a mukamin minista mai tsattsauran ra'ayin addini ne
- Sani ya ce ya na da ra'ayin rikau a addini da kuma siyasa bai kamata a ba shi mukami a gwamnati ba idan ana son zaman lafiya
- Ya ce mutumin da ya yi isgilanci ga Ubangiji a baya yanzu ya zama abin tausayi a wurin masu ba da mukami a kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi shagube ga wadanda majalisar Dattawa ta ki tabbatar da su a mukamin minista.
Sani ya ce akwai daya daga cikinsu da ya yi isgilanci ga Ubangiji yanzu ya zama abin tausayi kuma ya na neman alfarma a wurin sanatoci, Legit.ng ta tattaro.
Tsohon sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Talata 8 ga watan Agusta.
Sani ya ce bai kamata irin El-Rufai ya samu mukami a gwamnati ba
Sani ya ce daya daga cikinsu mai tsattsauran ra'ayin addini ne da siyasa da bai kamata ace ya na rike da mukamin gwamnati ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
"Wanda ba a tabbatar a minista ba, dan karami da ke son mulki a rayuwarsa wanda ya yi isgilanci ga Ubangiji yanzu ya zama abin tausayi a wurin masu ba da mukami.
"Mai tsattsauran ra'ayin addini da siyasa bai kamata ya samu mukamin gwamnati ba idan ana son zaman lafiya."
El-Rufai na daga cikin wadanda aka ki tabbatar da su a minista
Majalisar ta tabbatar da ministoci 45 yayin da ta dakatar da tabbatar da sauran mutane uku saboda korafe-korafen da ke kansu.
Wadanda aka dakatar din sun hada da Nasir El-Rufai daga jihar Kaduna da Stella Oketete daga jihar Delta sai Abubakar Sani Danladi daga jihar Taraba.
Nijar: Shehu Sani Ya Bukaci Sanatoci Su Yi Fatali Da Bukatar Tinubu
A wani labarin, sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya shawarci sanatoci da su duba girman bukatar Shugaba Tinubu da ya aike musu kan maganar Nijar.
Sani ya na magana ne kan bukatar Tinubu na tura dakarun soji zuwa Jamhuriyar Nijar.
Ya shawarci Shugaba Tinubu da kada ya bari turawan Yamma su zuga shi ya afkawa Jamhuriyar Nijar ba tare da duba abin ka iya zuwa ya dawo ba.
Asali: Legit.ng