MURIC Ta Bukaci Sanatoci Su Yi Bayanin Dalilin Kin Tabbatar Da El-Rufai Minista

MURIC Ta Bukaci Sanatoci Su Yi Bayanin Dalilin Kin Tabbatar Da El-Rufai Minista

  • Kungiyar MURIC ta bukaci cikakken bayani kan dalilin kin tabbatar da tsohon Gwamna, Nasiru El-Rufai a matsayin minista
  • Kungiyar ta bayyana haka ne bayan majalisar Dattawa ta ki tabbatar da El-Rufai a mukamin minista a jiya Litinin 7 ga watan Agusta
  • Ta ce tabbas wannan bai rasa nasaba da wasu da ke adawa da tikitin Musulmi da Musulmi saboda El-Rufai ya taka rawa wajen tallata Tinubu

FCT, Abuja - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta bukaci bahasi daga majalisar Dattawa kan kin tabbatar da Nasir El-Rufai a matsayin minista.

A ranar Litinin 7 ga watan Agusta ne majalisar ta tabbatar ministoci 45 daga cikin 48 amma banda El-Rufai da wasu mutum uku, PM News ta tattaro.

MURIC ta bukaci majalisa ta yi bayani kan kin tabbatar da El-Rufai a matsayin minista
Kungiyar MURIC Ta Bukaci Sanatoci Su Ba Da Dalilin Kin Tabbatar Da Tsohon Gwamna El-Rufai Mukamin Minista. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

MURIC ta zargi masu adawa da tikitin Musulmi da Musulmi

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

MURIC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar da sa hannun Farfesa Ishaq Akintola a yau Talata 8 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"A jiya majalisar Dattawa ta tabbatar da ministoci duka amma banda mutum uku, tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-rufai ya na daga ciki.
"Mutanen jihar Kaduna da kuma Musulmin Nijeriya ba su ji dadin haka ba na kin tabbatar da El-Rufai a matsayin minista."

MURIC ta ce wannan wani salo ne na daukar fansa a kan El-Rufai

Sanarwar ta kara da cewa:

"Abin da ke faruwa yanzu shi ne wadanda ke adawa da tikitin Muslimi da Muslimi su ne su ke son kawo cikas.
"Bai kamata a ce masu tantancewar sun mika wuya ga 'yan Shi'a da suka yi zanga-zanga a harabar majalisar kan hana El-Rufai mukamin minista ba."

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Na So Tinubu Ya Cire El-Rufai Cikin Ministocinsa, Sun Fadi Dalili

MURIC ta ce wannan wani salo ne na daukar fansa daga masu adawa da shi ke yi don ya hada kan Musulmin Arewa maso Yamma don zaban Tinubu, The Eagle Online ta tattaro.

Yadda Nasir El-Rufai, Danladi Da Okotete Su Ka Samu Tasgaro Wajen Zama Ministoci

A wani labarin, majalisar Dattawa ta gama tantance ministocin Shugaba Tinubu bayan gama tantance su.

Nasru El-Rufai da Danladi Abubakar da kuma Stella Oketete su ne mutum uku da majalisar ba ta tabbatar da su a matsayin minstoci ba saboda wasu dalilai.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio shi ya sanar da hakan bayan tabbatar da sunayen minstoci 45 daga cikin 48 da aka mika majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.