Cikakkun Sunayen Ministocin Da Majalisar Dattawa Ta Tabbatar, Jihohi Da Yankunansu
Majalisar dattawa ta tabbatar da wasu zababbun ministocin shugaban kasa Bola Tinubu bayan tantance su a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta.
Yayin zaman majalisar na ranar Litinin, Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa, ya sanar da tabbatar da mutane 45 cikin 48 da shugaban kasa Tinubu ya zaba, kamar yadda Legit.ng ta bibiyi shirin a NTA.
Yadda majalisar dattawa ta tantance zababbun ministocin Tinubu
Shugaban kasa Tinubu, ya mika sunayen zababbun ministoci 28 gaban majalisar dattawan a ranar 27 ga watan Yuli ta hannun shugaban ma'aikatan shugaban kasa kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
Bayan nan shugaban kasar ya mika sunayen wasu mutum 19 a ranar Talata, 1 ga watan Agusta, ciki harda tsoffin gwamnoni, Sanatoci, masu fasaha da masu yi wa jam'iyyar biyayya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Cikin wani yanayi mai cike da dirama, shugaban kasar ya rubuta wasika majalisar dattawa domin a janye sunan Maryam Shetty da kuma maye gurbinta da Mariya Mahmoud, bayan sukar da zabarta ya sha a soshiyal midiya sannan aka zabi Festus Keyamo a ranar Alhamis, 3 ga Agusta.
Hakan ya sa jimillar ministocin ya kama 48, amma majalisar dattawar ta tabbatar da 45 a ranar Litinin.
Ga jerin wadanda aka tabbatar, jihohi da yankunansu a kasa:
Yankin kudu maso kudu – mutum 7 nominees
- Ekperikpe Ekpo (Akwa Ibom)
- Betta Edu (Cross River)
- Heineken Lokpobiri (Bayelsa)
- John Enoh (Cross River)
- Festus Keyamo (Delta)
- Abubakar Momoh (Edo)
- Nyesom Wike (Rivers)
Yankin kudu maso gabas — 5
- Nkiru Onyejiocha (Abia)
- Uju Ohaneye (Anambra)
- David Umahi (Ebonyi)
- Uche Nnaji (Enugu)
- Doris Uzoka (Imo)
Yankin kudu maso yamma — 9
- Dele Alake (Ekiti)
- Tunji Alausa (Lagos)
- Lola Ade John (Lagos)
- Ishak Salako (Ogun)
- Bosun Tijjani (Ogun)
- Olawale Edun (Ogun)
- Olubunmi Tunji-Ojo (Ondo)
- Adegboyega Oyetola (Osun)
- Adebayo Adelabu (Oyo)
Yankin arewa maso gabas — 7
- Tahir Mamman (Adamawa)
- Yusuf M Tuggar (Bauchi)
- Ali Pate (Bauchi)
- Abubakar Kyari (Borno)
- Alkali Ahmed Saidu (Gombe)
- Uba Maigari Ahmadu (Taraba)
- Ibrahim Geidam (Yobe)
Yankin arewa maso yamma — 9
- Mohammed Badaru (Jigawa)
- Maryam Mairiga Mahmoud (Kano)
- Abdullahi T Gwarzo (Kano)
- Ahmad Dangiwa (Katsina)
- Hanatu Musawa (Katsina)
- Yusuf Tanko Sununu (Kebbi)
- Atiku Bagudu (Kebbi)
- Bello M Goronyo (Sokoto)
- Bello Matawalle (Zamfara)
Yankin arewa ta tsakiya — 8
- Joseph Utsev (Benue)
- Zephaniah Bitrus Jisalo (FCT)
- Shuaibu A Audu (Kogi)
- Lateef Fagbemi (Kwara)
- Imaan S-Ibrahim (Nasarawa)
- Mohammed Idris (Niger)
- Aliyu Sabi Abdullahi (Niger)
- Simon Lalong (Plateau)
Da Dumi-Dumi: FG Da NLC Sun Fara Tattaunawa Kan Shirin Rage Radadi Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito
Ganduje ya fadi dalilin rashin ba Kwankwaso kujerar minista
A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana dalilin rashin ganin sunan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso cikin jerin sunayen ministocin Tinubu.
A cikin satin da ya gabata ne dai Shugaba Tinubu ya aike da ragowar sunayen mutum 19 ga majalisar dattawa domin tantance su a matsayin ministoci.
Asali: Legit.ng