Mariya Bunkure ta Bayyana a Majalisa, Ta Canji Maryam Shetty a Sahun Ministoci

Mariya Bunkure ta Bayyana a Majalisa, Ta Canji Maryam Shetty a Sahun Ministoci

  • Sanatoci da-dama sun yaba da Shugaban kasa ya dauko Mariya Bunkure domin ta zama Ministan tarayya
  • ‘Yan majalisa sun yi mata tambayoyi a kan horas da dalibai, jarrabawar MDCN da annobar COVID-19
  • Bayan ta amsa tambayoyin, Sanatoci sun bukaci Dr. Bunkure ta tafi domin tantance Festus Keyamo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - A ranar karshe na tantance wadanda za su zama Ministoci, Mariya Mahmoud Bunkure ta isa zauren majalisar dattawan Najeriya.

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta bibiyi abubuwan da ke Wakana kai tsaye a majalisa, an tantance Dr. Mariya Mahmoud Bunkure da kimanin karfe 1:20.

Da aka gayyace ta domin ta bayyana kan ta, tsohuwar Kwamishinar ilmin shaida cewa ta gama digiri a ilmin likitanci daga jami'ar Bayero a Kano.

Majalisa
A Majalisar Dattawa ake tantance Ministoci Hoto: President of the Senate
Asali: Facebook

Mariya Mahmoud Bunkure tayi wa NYSC

Kara karanta wannan

Ministoci: Sanatoci sun Tantance Mutum 46, Jami’an Tsaro na Binciken Ragowar 2

Bayan gama digiri a shekarar 2005, Mariya Bunkure ta aikin bautan kasa watau NYSC a Filato.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya ce Ministar goben ta taso ne a gidan da ba su da hali, amma tayi kokari har ta iya zama Likita.

Kawu Sumaila da Barau Jibrin sun nuna cewa sun yi farin ciki da Mai girma shugaba Bola Tinubu ya zabi Dr. Bunkure domin ya ba ta mukami.

Likita abin alfaharin Kanawa

An rahoto Mataimakin shugaban majalisar ya na mai alfahari da wannan kamila, ya ce zai so ‘ya ‘yansa su yi koyi da irin hali da dabi’arta a nan gaba.

Sanata Kawu Sumaila wanda ya fadawa majalisa cewa mutanen Kudancin Kano da yake wakilta sun ji dadin jin labarin bada sunan daya daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

Rufai Hanga mai wakiltar Kano ta tsakiya ya nuna ya na goyon bayan Bunkure, hakan ya nuna duka ‘yan majalisar jihar Kano sun yi na’am da ita.

An watso jerin tambayoyi

Sanatocin da su ka jarraba basirar likitan yayin da ake tantance ta sun hada da: Osita Izunaso, Muhammad Tahir Mungono, Tony Nwoye da Dave Umahi.

Sanatoci sun yi tambayoyi a kan annobar coronavirus, jarrabawar likitoci da ra'ayinta game da wajabtawa dalibai darasin tarihi a makarantu.

Mariya Bunkure ta kawo misali da ayyukan da su ka yi a gwamnatin Abdullahi Ganduje. A karshe ‘yan majalisa su ka sallame ta bayan sun gamsu.

An cire Maryam Shetty

A baya kun ji masu bibiyar Twitter sun ce Maryam Shetty ta fi tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle cancanta ta fuskar ilmin boko da sanin aiki.

Wasu sun ce idan Shugaban kasa Bola Tinubu yana so ya cire sunan wani a Ministocinsa, Bello Matawalle ne ba wannan mata daga Jihar Kano ba.

Kara karanta wannan

Ganduje Sun Yi Wa Maryam Shetty Izgili a Bidiyo Bayan ‘Tunbuke’ Ta a Jerin Ministoci

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng