Atiku bai Hakura ba, Ya Sake Maka Tinubu a Kotun Kasar Amurka a Kan Zargi Mai Karfi
- Atiku Abubakar ya yi bayanin abin da ya faru a shari’ar da yake so ya yi da Bola Tinubu a Amurka
- Wazirin Adamawa ya fitar da jawabin da ya yi cikakken karin haske ta bakin Mista Phrank Shaibu
- Alhaji Atiku ne ya janye karar da ya kai, ya bukaci a saurari shari’ar a wata babban kotu a Illinois
Abuja - Phrank Shaibu ya sanar da cewa Mai gidansa, Atiku Abubakar ya kumakarar Bola Tinubu a wani kotun lardin Arewacin Illinois a kasar Amurka.
Kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna, Mai taimakawa ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PDP a 2023, Phrank Shaibu ya ya ce kara na kotu.
Atiku Abubakar ya na sa ran ba dadewa ba Alkali ya saurari karar mai lamba; 23-5099 (N. D. III.).
Atiku ya janye karar farko
Ba komai ya jawo ‘dan takaran shugabancin Najeriyan ya janye karar farko da ya shigar a kasar wajen ba, Mista Shaibu ya ce illa sabuwar karar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Atiku Abubakar ya janye karar da ke gaban kotun Cook County, Illinois County a Amurka ne saboda ya kai karar zuwa wani babban kotu.
Sannan ya zo ne ayi shari’ar ba tare da sabawa ka’idar kotu ba, saboda haka yanzu aka fara shari’ar.
- Phrank Shaibu
"Da walakin, goro a miya"
A jawabin da Hadimin na Atiku Abubakar ya fitar a karshen makon da ya gabata, ya ce ya na kalubalantar takardun shaidar karatun shugaban kasar.
Wazirin Adamawa ya ce akwai alamar tambaya game da makarantun da Tinubu yake ikirarin ya halarta tun daga firamarensa, sakandare zuwa jami’a.
Leadership ta ce ‘Dan siyasar ya ce saboda haka har yau ba a taba samun abokin karatun Tinubu a Duniya ba, sai dai a ga abokansa a harkar siyasa.
"A shekarun baya, tsofaffin shugabanni sun gayyaci abokan karatunsu zuwa Aso Rock Villa.
Ko Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin abokan karatunsa a Katsina Middle School. Amma wa Tinubu ya gayyata zuwa fadar shugaban kasa?
Tinubu zai kafa Gwamnati
Ku na da labari Mai girma Shugaban kasar Najeriya zai nada Ministoci 48, adadin da ya zarce tarihin da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa a 2019.
Tsofaffin Gwamnonin jihohi 9 ne aka zaba a cikin Ministoci. A karon farko a tarihi an samu Minista daga birnin Abuja, kuma mata 9 za su zauna a FEC.
Asali: Legit.ng