Hotuna: 'Yan ajinsu shugaba Buhari sun kai masa ziyara a Daura, har daya ya yi masa kyautar ba-zata

Hotuna: 'Yan ajinsu shugaba Buhari sun kai masa ziyara a Daura, har daya ya yi masa kyautar ba-zata

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakuncin 'yan ajinsu a gidansa dake Daura a jihar Katsina yayin bikin babbar sallah
  • Kamar yadda Buhari Sallau, hadimin shugaban kasan ya bayyana, mutum 14 ne suka kai masa ziyarar har da mace daya, Hajiya Binta 'Yar Malele
  • Ya kara da bayyana cewa, daya daga cikin 'yan ajinsu, Sanata Abba Ali ya gwangwaje shugaban kasan da kyautar girmamawa

Daura, Katsina - A ranar Talata, 12 ga watan Yulin 2022, 'yan ajin su shugaban kasa Muhammadu Buhari sun kai masa ziyara tare da gaisuwar sallah a gidansa dake Daura ta jihar Katsina.

'Yan ajinsu shugaban kasan wadanda dukkansu sun manyanta, sun kai masa gaisuwa cike da girmamawa inda suka yi hirar yaushe gamo.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya fito yana adawa da takarar Musulmi-Musulmi

Baba Buhari and his classmates
Hotuna: 'Yan ajinsu shugaba Buhari sun kai masa ziyara a Daura, har daya na yi masa kyauta ba-zata
Asali: Instagram

Kamar yadda hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau ya wallafa a shafinsa na Instagram ya lissafo sunayensu har su goma sha hudu.

"Shugaban kasan ya karba bakuncin Sanata Abba Ali,Hajiya Binta 'yar Malele, Alhaji Hassana Sada HK, Alhaji Abdulmalik KB, Muntari Abubakar Mashi, Adamu Magaji Bakori, Muhammadu Kabir Daura, Yunusa I. Saulawa, Alh Abdu IBR Maigora, Bawa Musawa, Salmanu Darma, Garba Kafur da Amadu Yahaya Alti yayin shagalin bikin sallah."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa, "Shugaban kasa ya karba kyauta daga Sanata Abba Ali"

AGF Malami yayi wuff da diyar shugaba Buhari, hotuna suna bayyana

A wani labari na daban, a ranar 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Nana Hadiza Muhammadu Buhari da AGF Abubakar Malami, SAN.

An daura auren a Abuja yayin da aka yi karamin biki a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake Abuja tare da 'yan uwa da abokan arziki.

Kara karanta wannan

2023: Cikakkun sunayen dakarun Tinubu da za su kawo masa kujerar shugaban kasa

Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan.

"Eh, da gaske ne, antoni janar na tarayya ya aura diyar shugaban kasa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel