Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Amince da Nadin Kwamishinoni 18
- Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tantance tare da tabbatar da naɗin sabbin kwamishinoni 18 da gwamna Dauda Lawal ya aiko mata
- Mambobin majalisar sun yi aikin tantance mutanen ne a zamansu na ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, 2023
- Tun da farko gwamna Dauda Lawal ya aike da sunayen mutum 18 ga majalisar domin tantance su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Zamfara State - Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tantance tare da tabbatar da naɗin mutane 18 da Gwamna Dauda Lawal ya aika mata a matsayin kwamishinoni.
Jaridar Vangaurd ta tattaro vewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na majalisar, Malam Nasiru Biyabiki ya fitar a Gusau ranar Alhamis.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa a kwanakin baya ne majalisar dokokin jihar ta 7 ta sanar da karbar mutane 18 da Lawal ya naɗa a kwamishinoni.
Kakakin majalisar dokokin ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“An tantance wadanda gwamna ya nada kuma an tabbatar dasu a zauren majalisar da ke Gusau ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, 2023."
Jerin sunayen sabbin kwamishinonin da majalisar da tabbatar
Nasiru Buyabiki ya bayyana sunayen sabbin kwamishinonin da majalisar da amince da naɗinsu ranar Alhamis, ga su kamar haka;
1. Sule Adamu
2. Salisu Musa
3. Kabiru Birnin-Magaji
4. Yau Haruna-Bakura
5. Abdurrahman Tumbido
6. Lawali Barau
7. Nasiru Ibrahim
8. Tasiu Musa
9. Mannir Haidara
10. Kyaftin Bala Mairiga mai ritaya
11. Abdul’aziz Sani (SAN)
12. Ahmed Yandi
13. Wadatau Madawaki
14. Aisha Anka
15. Bello Auta
16. Abdulmalik Gajam
17. Mahmud Muhammad
18. Dakta Nafisa Maradun.
Tun da farko, shugaban masu rinjaye na majalisar, Malam Bello Mazawaje (APC – Tsafe ta Gabas) ya gabatar da kudirin a kan bukatar gwamnan na tantancewa tare da tabbatar da sunayen wadanda ya naɗa.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Malam Aliyu Ango (APC – Talata-Mafara ta Kudu) ne ya goyi bayan kudurin, kamar yadda PM News ta rahoto.
Nijar: "Kada Ka Jefa Yankin Sahara Cikin Yaƙi" Sheikh Rijiyar Lemu Ga Tinubu
A wani labarin kuma Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya buƙaci shugaba Tinubu ya guje wa ɗaukar matakin soji kan gwamnatin sojin Nijar.
Malamin ya ce ya kamata Najeriya ta yi tunani a kan dangantakar da ke.tsakaninta da ƙasar da kuma al'ummar jamhuriyar Nijar.
Asali: Legit.ng