Mariya Mahmoud: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wacce Ta Maye Gurbin Maryam Shetty Daga Kano

Mariya Mahmoud: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wacce Ta Maye Gurbin Maryam Shetty Daga Kano

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya maye gurbin matashiya Maryam Shetty daga Kano da sunan Dakta Mariya Bunkure a mukamin minista
  • Tinubu ya sauya sunan tare da mika wa zuwa majalisar Dattawa a yau Juma'a bayan Maryam Shetty ta isa Abuja don tantancewa
  • Mutane da dama sun yi ta korafe-korafe kan nada Maryam Shetty inda suke ganin ba ta cancanta ba a matsayin minista

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Dakta Mariya Mahmud Bunkure ta samu shiga jerin sunayen ministocin Tinubu a yau Juma'a 4 ga watan Agusta.

Mariya ta samu shiga ne bayan Shugaba Tinubu ya sauya sunan Maryam Shetty a yau Juma'a 4 ga watan Agusta.

An sauya sunan Maryam Shetty da Dakta Mariya a mukamin minista a Kano
Dakta Mariya Mahmoud Ta Maye Gurbin Maryam Shetty A Mukamin Minista Daga Kano. Hoto: YouTube.
Asali: Twitter

An gano wani faifan bidiyo inda Maryam Shetty ta isa harabar majalisar kafin sauya sunanta da na Dakta Mariya da safiyar yau.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Gaskiya Ta Bayyana Kan Ainihin Dalilin Cire Sunan Maryam Shetty

Mariya Mahmud ita ce tsohuwar kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar Kano lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje, kamar yadda Wikipedia ta bayyana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta tattaro muku abubuwan da ya kamata ku sani game da Dakta Mariya Mahmoud Bunkure.

1. Mahaifa

An haifi Dakta Mariya a garin Bunkure da ke cikin jihar Kano a Arewacin Najeriya, Platinum Times ta tattaro.

2. Mukamin kwamishina

Tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada Dakta Mariya Bankure a matsayin kwamishinan a ma'aikatar ilimi mai zurfi a lokacin gwamnatinsa.

3. Mukamin Minista

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zabi Dakta Mariya a matsayin minista a yau Juma'a 4 ga watan Agusta bayan sauya sunan Maryam Shetty daga jihar Kano.

4. Bude makarantu

Bayan shafe watanni 7 da kulle manyan makarantu a jihar saboda cutar Corona da ta addabi duniya, Dakta Mariya ta ayyana 26 Oktoba 2020 a matsayin ranar bude manyan makarantu a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Muhimman Abubuwa 5 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Maryam Shetty Da Tinubu Ya Sauya Sunanta A Jerin Ministoci

Tinubu Ya Mika Sunayen Sabbin Ministoci 19, Lalong, Matawalle Sun Samu Shiga

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya tun farko ya mika sunayen ministoci 28 ga majalisar Dattawa yayin aka gama tantance su.

A ranar Laraba 2 ga watan Agusta Tinubu ya sake tura sunayen ministoci 19 ga majalisar don tantancewa, yayin da wasu tsoffin gwamnoni suka samu shiga da suka hada da na Zamfara da Kebbi da Plateau.

Daga cikin ministoci 19, an sauya sunan Maryam Shetty da Dakta Mariya Mairiga tare da kara sunan Festus Keyamo a jerin sunayen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.