Bola Tinubu Ya Kafa Wasu Sababbin Tarihi 5 a Najeriya Wajen Nadin Ministocinsa

Bola Tinubu Ya Kafa Wasu Sababbin Tarihi 5 a Najeriya Wajen Nadin Ministocinsa

  • Daga 1999 zuwa shekarar nan, ba a taba yin lokacin da aka samu mutane 47 sun zama Ministoci ba
  • Akwai yiwuwar a gwamnatin Bola Tinubu, mutane fiye da 42 su rike kujerar Minista a lokaci guda
  • Wani tarihi da za a kafa shi ne mutanen Abuja sun samu Minista, jihar Ogun ta na da kujeru 3 a FEC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tun daga shekarar 1999 da aka dawo mulkin farar hula zuwa yau, ba a taba samun wani shugaban Najeriyan da ya nada Ministoci 43 ba.

Muhammadu Buhari ne kadai ya taba kai adadin Ministoci su ka zama 42 wa’adinsa na biyu, The Cable ta ce za a karya wannan tarihi a yanzu.

Adadin mutanen da Bola Tinubu yake so su zama Ministoci a gwamnatinsa shi ne 47, karin mutum biyar a kan wadanda su ka bar ofis a Mayu.

Kara karanta wannan

An Taso Tinubu, Ana Neman a Cire Tsohon Gwamna Daga Ministoci Kamar Shetty

Ministocin Gwamnati
Shugaba Bola Tinubu zai nada Ministoci 47 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministoci 47 a lokaci daya

A makon jiya Mai girma Shugaban kasa ya bada sunayen mutane 28 da ake sa ran za su zama Ministoci, a makon nan sai ya karo jerin wasu 19.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zuwa jiya an tantance ‘yan sahun farko, zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta gama aikinta, za a iya samun mutane 47 da za su zama Ministoci.

A lokacin da Goodluck Jonathan ya shiga ofis a 2011 ya zabi mutane 33 a Ministocinsa.

Shi kuwa Marigayi Umaru Yar’Adua ya nada mutum 39 ne kamar yadda Olusegun Obasanjo ya fara da mutane 42, daga baya ya rage masu yawa.

Minista daga Abuja

Wani tarihi da Bola Tinubu ya kafa shi ne ba mutanen Abuja kujerar Minista a wannan karo.

Rahoto ya zo cewa tsohon ‘dan majalisar wakilai, Zephaniah Jisalo yana cikin wanda za a tantance a jerin karshe na sunayen Ministocin da aka mika.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Murkushe Arewa Tun Wajen Nada Ministoci

Ministoci 3 daga Ogun

Mutum uku za su wakilci Ogun a FEC – Wale Edun, Bosun Tijjani da Ishak Salako. Bauchi, Katsina, Kano, Taraba, K/Riba da Adamawa su na biyu.

...Mata 9 za su zauna a FEC

A lokacin ‘Yaradua ne mata bakwai su ka zama Ministoci, wannan karo ana sa ran za a rantsar da mata bakwai a lokaci daya, watakila ba a taba haka ba.

Lola Ade-John wanda ta yi aiki a bankuna da Maryam Shettima su na cikin matan da aka dauko.

Tsofaffin Gwamnoni 10

Idan an tashi kafa gwamnati, an ji labari cewa za a sau tsofaffin Gwamnoni irinsu Nasir El Rufai, Badaru Abubakar da kuma Ezenwo Nyesom Wike

An bada sunan David Umahi a cikin Ministoci. Yanzu an kara da Simon Lalong Bello Matawalle da kuma Atiku Abubakar Bagudu, za su zama 10 kenan.

Zamanin Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta tuna da yadda Muhammadu Buhari ya nada Ministoci 36 a 2015. Tsofaffin Gwamnoni a FEC ba su taba kai goma a lokacinsa ba.

Kara karanta wannan

Binani, Keyamo, Fashola Da 'Yan Siyasa 10 Da Ba Su Da Rabon Zama Ministoci

Daga baya adadin Ministocin tarayyan ya ragu bayan rasuwar James Ocholi, aka dauki tsawon lokaci ba tare da Kogi ta samu wakilci a FEC ba.

Daga baya Amina J. Mohammed ta ajiye kujerarta da ta samu mukami a majalisar dinkin Duniya, daga baya Ibrahim Usman Ibril ya zama Sarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng