Wasu Ministocin Shugaban Buhari da ba a jin duriyar su a Gwamnati
Wannan karo mun kawo maku wani dogon jeri na wasu Ministocin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ba a jin labarin su a Gwamnatin nan. Wasu Ministocin dai na yawan fitowa cikin labarai bini-bini amma dai wasu shiru ka ke ji.
Ga dai wadannan Ministoci nan mun kawo:
1. Usaini Uguru Uguru
Ministan Neja-Deltan Najeriya yana cikin wadanda ba a jin labarin su da aikin da su ke yi. Kwanakin baya dai mun ji cewa Jam’iyyar APC a Jihar Kuros-Riba ta dakatar da Ministan.
2. Sulaiman Adamu Kazaure
Sulaiman Kazaure wanda shi ne Ministan harkokin ruwa na Najeriya dai shi ma yayi shiru cikin ‘yan kwanakin nan.
3. Bawa Bwari Abubakar
Hon. Bawa Bwari Ministan da ya fito daga Jihar Neja shi ma yayi kusufi. Karamin Ministan ma’adanan kasar yayi nisan kiwo.
4. Ibrahim Jibril
An dade ba a jin labarin Ministan muhalli na kasar Jibril ba. Bayan tafiyar Amina Mohammed Majalisar dinkin Duniya Jibril ne ya karbi aikin ta.
5. Omole Daramola
Kamar dai Mai-gidan sa Fasto Usaini Uguru, shi ma karamin Ministan na harkokin Neja-Delta Daramola ba a jin labarin sa ko a makwabta.
6. Anthony Onwuka
Farfesa Onwuka shi ne karamin Ministan ilmi na kasar kuma shi ma ba a jin duriyar sa. Kwanaki dai Ministan yayi ta fama da rashin lafiya.
7. Heineken Lokpobiri
Ana bukatar a fara cigiyar daya daga cikin Ministan gona na kasar Lokpobiri. Kwanaki dai an ji Ministan yayi kaca-kaca da Gwamnan Jihar sa ta Bayelsa.
8. Osagie Ehanire
Wasu ma dai sun fara manta wanene karamin Ministan lafiya na kasar. A kwanakin baya ma dai sai dai aka ji labari cewa Ma’aikatan kasar na neman a tsige Ministan.
9. Sulaiman Hassan
Tun da Sulaiman Hassan ya canji Amina Mohammed daga Jihar Gombe dai har yau ba a wani ji labarin aikin da yake yi ba. Hassan yana cikin masu taimakawa Minista Raji Fashola.
10. Stephen Ocheni
Shi ma Farfesa Stephen Ocheni ba a jin labarin sa tun lokacin da Yemi Osinbajo ya rantsar da shi lokacin yana Mukaddashin Shugaban kasa a bara bayan rasuwar James Ocholi.
Haka zalika dai Karamar Ministar kasuwanci ta kasar Aisha Abubakar da Takwarar ta ta harkokin kasar waje Khadija Bukar Abba Ibrahim su na cikin wadanda ba a jin ko labarin su a kasar a Gwamnatin nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng