Yanzu-yanzu: Minista a gwamnatin Buhari ya yi murabus

Yanzu-yanzu: Minista a gwamnatin Buhari ya yi murabus

- Ministan muhallin Buhari ya yi murabus

- Shine ministan muhalli na biyu da yayi murabus a gwamnatin Buhari

Ministan muhalli, Ibrahim Usman Jibrin, ya yi murabus daga kujeransa. Ya gabatar da takardan murabus dinsa ne a ranan Laraba yayin zaman majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada, Ibrahim Usman Jibrin, a matsayin karamin ministan muhalli ne a watan Disamban 2015.

Ya bayyana cewa ya yi murabus ne bisa ga sabuwar mukamin da ya samu na sarauta a jihar Nasarawa.

Yanzu-yanzu: Minista a gwamnatin Buhari ya yi murabus
Yanzu-yanzu: Minista a gwamnatin Buhari ya yi murabus
Asali: Facebook

Mun kawo muku cewa an shiga taron FEC na Majalisar zartarwa na Tarayya. Shugaba Muhammadu Buhari yayi abin da ya ba kowa dariya a wajen taron bayan yayi ido-biyu da daya daga cikin manyan Ministocin sa.

Jama’a sun kece da dariya a lokacin da aka zauna wajen taron yau inda Shugaban Kasar ya nemi Ministan muhalli na Najeriya watau Ibrahim Usman Jibril ya bude taron da addu’a. Buhari ya kira Ministan na sa ne da Mai Martaba.

A makon da ya gabata ne Ibrahim Jibril ya samu sarautar Kasar Nasarawa a cikin Jihar ta Nasarawa. Wannan ya sa Shugaban kasar ya kira Ministan da Mai Martaba a lokacin da za a soma taron Majalisar Ministoci na wannan makon.

KU KARANTA: Jami'an tsaro ke mayar hannun agogon yaki da Boko Haram baya, suna kai musu abinci da man fetur

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, Sabon Sarki Ibrahim Jibril ne ya bude taro da addu’a, yayin da karamin Ministan lafiya Osagie Ehanire yayi wata addu’ar a madadin sauran Kiristocin da ke cikin Majalisar Tarayyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng