Tantance Ministoci: Rudani Yayin Da Akpabio Ya Hana Alake Rera Taken Najeriya A Majalisa

Tantance Ministoci: Rudani Yayin Da Akpabio Ya Hana Alake Rera Taken Najeriya A Majalisa

  • Daya daga cikin ministocin da aka nada don tantancewa, Dele Alake ya samu kariya yayin da majalisa ta hana shi yin taken Najeriya
  • Alake na daga cikin ministocin da Tinubu ya zaba duk da kasancewar shi mai ba shi shawara na musamman a fannin yada labarai
  • Sanata Simon Davou daga jihar Plateau shi ya bukaci Alake ya karanto taken Najeriya na biyu yayin tantance shi a majalisar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – An samu hatsaniya a majalisar Dattawa yayin tantance ministoci inda shugaban marasa rinjaye, Sanata Simon Davou ya bukaci wanda ake tantancewa, Dele Alake ya karanto taken Najeriya na biyu.

Alake, wanda shi ne mai ba wa Shugaba Tinubu shawara a fannin yada labarai ya halarci majalisar don tantance shi kamar sauran ministoci inda aka masa tambayoyi a fannin al’adu da yada labarai.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: A Karshe, Akpabio Ya Karanto Sunayen Ragowar Ministocin Da Za a Nada

Majalisa ta hana Alake karanta taken Najeriya yayin tantance shi minsta a Abuja
A Yayin Tantance Ministoci, Sanata Ya Tambayi Alake Ya Karanto Taken Najeriya. Hoto: Imran U Wakili (PULLO).
Asali: Facebook

Alake ya kasance hadimin Tinubu a fannin yada labarai

An bayyana Alake a matsayin wani gwarzo ba a jihar Lagos kadai ba har kasa baki daya musamman gwagwarmayar kawo mulkin farar hula a lokacin mulkin soja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Davou, wanda ke wakiltar Plateau ta Arewa bayan ya yabi Alake ya kuma bukace shi da ya karanto taken kasar na biyu, Daily Trust ta tattaro.

Yayin kare Alake, shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Obayemi Bamidele da ke wakiltar Ekiti ta Tsakiya ya roki shugaban majlisar, Godswill Akpabio da ya umarci Alake ya risina ya wuce.

Akpabio ya kare Alake kan yin taken Najeriya a majalisar

Wannan bayani na Opeyemi ya jawo kace-nace yayin da Godswill Akpabio ya tsoma baki da cewa:

“Ko ni nan a matsayi na babba zan iya karanta duk wani bangare na taken Najeriya.”

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Sanatan Kogi Ya Nemi Tayarwa Da El-Rufai Hankali Yayin Tantacewa a Majalisa

Majalisar ta hana Alake karanto taken kasar tare da umartan shi da ya risina a gaban majalisar ya wuce, kamar yadda Platinum ta ruwaito.

Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina Ta Sha Kuka Gaban Sanatoci Bayan Ta Tuna Mahaifinta

A wani labarin, daya daga cikin ministocin da ake tantancewa daga jihar Katsina, Hannatu Musawa ta sharbi kuka bayan tuno da mahaifinta.

Hannatu ta bayyana a gaban Sanatoci inda ta ke ba da tarihin rayuwarta da yadda mahaifinta ya sha wahala don ganin ta samu ingantacciyar rayuwa.

Musawa ta ce ta na jin bakin ciki yadda mahaifin nata ba zai ga wannan rana ba da ake tantance ta a matsayin minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.