Peter Obi Ya Shiga Rudani Yayin Da Ya Nemi Wayoyinsa 2 Ya Rasa A Kotu, Bidiyon Ya Yadu

Peter Obi Ya Shiga Rudani Yayin Da Ya Nemi Wayoyinsa 2 Ya Rasa A Kotu, Bidiyon Ya Yadu

  • A cikin wani faifan bidiyo, an gano dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi cikin rudani
  • Obi ya halarci kotun sauraran kararrakin zabe inda ya nemi wayoyinsa guda biyu ya rasa cikin firgici
  • Dan takarar ya samu rakiyar mataimakinsa, Dakta Datti Baba Ahmed tare da wasu magoya bayansu zuwa kotun

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya shiga rudani bayan ya manta inda ya ajiye wayoyinsa guda biyu.

Obi ya halarci kotun sauraran kararrakin zabe a Abuja tare da mataimakinsa, Datti Baba Ahmed da wasu mutane, Legit.ng ta tattaro.

Peter Obi ya shiga rudani yayin da ya rasa wayoyinsa biyu 2 a kotu
Dan Takarar Shugaban kasa, Peter Obi Yayin Neman Wayoyinsa A Kotu. Hoto: TheCable.
Asali: Twitter

An gano yadda Obi ya rikice bayan ya rasa wayoyinsa a kotu

A wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an gano Peter Obi cikin tashin hankali yayin da ya ke neman wayoyin nasa.

Kara karanta wannan

Ta Rikice a Nijar, Masu Zanga-Zanga Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya na fada wa Datti Baba Ahmed da ke bukatar sanin me ya ke faruwa, cewa ya zo nan da wayoyi guda biyu kuma bai gansu ba.

Ya ce:

"Na zo da wayoyi guda biyu cikin nan."

Daga baya TheCable ta tabbatar cewa an samu wayoyin na Peter Obi bayan an yi bincike.

Obi na kalubalantar zaben Tinubu da aka yi a watan Faburairu

Obi ya kasance na uku bayan sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ya shigar da kara tare da sauran 'yan takarar jam'iyyu musamman PDP, Atiku Abubakar don ganin an bi musu kadunsu.

Suna kalubalantar takarar shugaban kasa, Bola Tinubu da aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zabe da korafe-korafe da dama a kan halascin takarar Tinubu.

Kara karanta wannan

Wike Ya Shiga Rudani Tun Lokacin Da Tinubu Ya Nada Shi Minista

Kotu Zata Yanke Hukunci A Karar Da Peter Obi Ya Kalubalanci Zaben Tinubu

A wani labarin, kotu za ta yanke hukunci a kan karar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya shigar.

Obi na kalubalantar sahihancin zaben Bola Tinubu kan korafe-korafe da dama da suka hada da magudin zabe da sauran korafe-korafe.

Shugaban kwamitin alkalai 5, Alkali Haruna Tsammani, ya ce nan ba da jimawa ba zasu fadi sakamakon hukuncin da suka yanke ga kowane bangare ranar yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.