Zama Ministoci: Abin da Zai Faru da El-Rufai, Wike, Umahi a Majalisa – Tsohon Minista

Zama Ministoci: Abin da Zai Faru da El-Rufai, Wike, Umahi a Majalisa – Tsohon Minista

  • Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisa sunayen Ministocinsa, a makon nan ake sa ran tantance su
  • Da alamun za a tantance tsofaffin Gwamnoni da ‘Yan Majalisa su zama Ministoci cikin ruwan sanyi
  • Adeseye Ogunlewe ya yi bayani game da tantance wadanda Bola Tinubu yake so su zama Ministoci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Adeseye Ogunlewe ya ce tsofaffin gwamnonin jihohi da kuma tsofaffin ‘yan majalisa ba za su gamu da cikas wajen zama Ministoci ba.

Idan an tashi tantance zababbun Ministoci a majalisar dattawa, Adeseye Ogunlewe ya shaidawa tashar Channels, abin zai zo da sauki ga wasu.

Tsohon Ministan ayyuka da gidajen yana ganin wadanda sun rike jihohi da tsofaffin ‘yan majalisa za su zama Ministoci ba tare da yin gumi ba.

Ministoci
Nasir El-Rufai da Nyesom Wike za su zama Ministoci Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

A cikin wadanda aka zaba akwai tsofaffin Gwamnoni da wadanda yanzu haka su na majalisa ko sun taba zama ‘yan majalisar tarayya a tarihinsu.

Kara karanta wannan

Malaman Addinin Musulunci a Arewa Sun Roki a Hana El-Rufai Yin Minista, Sun Bayyana Dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin Gwamnoni da 'Yan Majalisa

A tsofaffin gwamnonin da ake sa ran a tantance a makon nan akwai Nyesom Wike, Nasir El-Rufai, David Umahi, Badaru Abubakar da Sani Danladi.

Abubakar Kyari, John Eno da Nkiruka Onyejiocha za su fuskanci abokan aikinsu a wajen tantancewar.

Hasashen Sanata Adeseye Ogunlewe

"Bari mu raba wadanda aka zaba zuwa gida dabam-dabam. Wasu sun yi aiki a majalisa a baya, akwai Sanatoci da kuma ‘yan majalisar tarayya.
A tunani na, za su samu tantacewarsu cikin gaggawa domin haka al’adarsu take, ba za su dade ba.
Sannan mu na da tsofaffin gwamnoni hudu, biyu daga ciki Sanatoci ne. Za a tantance su da wuri, ya rage ga sababbin shiga, su ne za a tasa a gaba."

- Adeseye Ogunlewe

Abin ba zai zo da wahala ba

Punch ta rahoto ‘dan siyasar yana hasashen abubuwa su zo da sauki domin wadanda aka kawo sunayensu wakilan jam’iyya ne da ake so a ba mukami.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Jerin Mutum 10 da Za a Saurari Sunayensu a Sahun Karshe na Ministoci

Bugu da kari, tun da har jami’an tsaro da hukumar EFCC sun tantance su, Ogunlewe yana ganin da wahala a samu matsala wajen tabbatar da Ministocin.

Muhammadu Sanusi II zai dawo?

Dazu mu ka ji labari an ga hotunan Muhammadu Sanusi II tare da na Shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabiru Yusuf a gidan gwamnatin Kano

A maimakon Mai martaba Aminu Ado Bayero, sai ga hoton Sarkin Kano na 14 da ake rade-radin za a maida kan karaga idan jam’iyyar NNPP ta karbi mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng