Mata 7 Daga Jihohin Katsina, Imo, Abia da Anambra da ke Shirin Zama Ministoci
- Mata 7 su ka samu shiga cikin sahun farko na Ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar a yau
- Ana kukan cewa mata ba su samun manyan mukaman siyasa da na kujerun gwamnati a Najeriya
- Zuwa yanzu mata su na da 25% na mukaman Ministocin da ake so a bada a gwamnatin Tinubu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wannan rahoto ya dauko sunayen duka matan da aka aikawa majalisar dattawa sunayensu:
1. Hannatu Musawa
Hannatu Musawa ta rike mataimakiyar mai magana da yawun bakin kwamitin PCC da Bola Tinubu yake neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Wannan lauya tayi gado ne domin mahaifinta shi ne Musa Musawa. Yanzu haka ta na cikin masu ba shugaban kasa shawara, ta na da digiri akalla shida.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Dr. Betta Edu
Dr. Betta Edu ta na cikin shugabannin APC na kasa da za su shigo gwamnati, likitar mai shekara 36 ta yi Kwamishinar lafiya a Jihar Kuros Ribas.
3. Dr. Doris Uzoka-Anite
Doris Uzoka-Anite tsohuwar Kwamishinar tattalin arziki ce a jihar Imo, kwararriyar ma’aikaciyar banki ce wanda tayi fice a mata a ilmin kudi.
4. Hon. Nkeiruka Onyejeocha
Ana sa ran Nkeiruka Onyejeocha za ta koma gwamnati, wannan karo a matsayin Minista bayan rasa kujerar majalisa a bana a dalilin LP a Abia.
5. Stella Okotette
Wata mace da za a tantance a majalisar dattawa domin zama Minista ita ce Stella Okotete. Muhammadu Buhari ya fara nada ta shugabar bankin NEXIM.
6. Uju Kennedy-Ohaneye
Wanda za ta wakilci Anambra a FEC ba kowa ba ce sai Kennedy-Ohaneye. ‘Yar kasuwar ta tsaya takarar shugaban kasa tare da Bola Tinubu a APC.
7. Iman Suleiman Ibrahim
Daga Nasarawa, Bola Tinubu ya bada sunan Iman Sulaiman-Ibrahim wanda ta jagoranci NAPTIP a baya, Iman mai digiri uku ta gama jami’a ta na 19.
El-Rufai Na Iya Zama Ministan Wutar Lantarki Yayin da Jerin Sunayen Ministoci Ya Isa Gaban Majalisar Dattawa
Tsofaffin Gwamnoni za su zama Ministoci
Ana da labari Hadiman shugaban kasa kamar Hannatu Musawa, Dele Alake da Olawale Edun za su zama Ministoci idan aka tantance su a majalisa.
Jerin sababbin Ministoci yana dauke da tsofaffin gwamnonin jihohi irinsu Badaru Abubakar, Ezenwo Nyesom Wike, David Umahi da Nasir El Rufai.
Asali: Legit.ng