Zan Cigaba da Kare Martabar Dimokradiyya, Shugaba Bazoum Bayan Sojoji Sun Masa Juyin Mulki
- A jiya Laraba ne 26 ga watan Yuli aka wayi gari da samun yunkurin juyin mulki a kasar Nijar da Mohamed Bazoum ke jagoranta
- Ana zargin wasu daga cikin masu tsaron Bazoum ne suka killace shi tare da hana komai tafiya a fadar shugaban kasar
- Daga bisani sun fitar da wata sanarwa inda suka kifar da gwamnatin Bazoum tare da wargaza duk wasu hukumomin gwamnati
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Niamey - Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya sha alwashin kare martabar dimukradiyya bayan sojoji sun tumbuke shi daga mulki.
Bazoum ya bayyana haka ne a kafar sadarwa a yau Alhamis 27 ga watan Yuli kwana daya bayan an masa juyin mulki a kasar.
Ministan harkokin wajen kasar, Hassoumi Massoudou shi ma ya yi martani a shafinsa na Twitter inda ya bukaci ‘yan dimukradiyya da masu kishin kasa su lalata shirin sojojin.
Yadda sojoji suka yi juyin mulki a Niger
Sanarwar ta su na zuwa ne bayan sojojin da suka yi juyin mulkin sun fitar da sanarwar kifar da gwamnatin Bazoum da wargaza duk hukumomin gwamnati a daren Laraba 26 ga watan Yuli.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan juyin mulki shi ne na bakwai a Afirka ta Yamma da ta Tsakiya tun shekarar 2020, The Guardian ta tattaro.
Da safiyar Laraba 26 ga watan Yuli ne wasu daga cikin masu tsaron Bazoum suka killace shi a fadar shugaban kasa da hakan ya jawo cece-kuce daga shugabannin kasashe daban-daban.
Har zuwa yau ana rike da Bazoum tare da kafa dokar ta baci
Massoudou ya tabbatar da cewa har zuwa safiyar ranar Alhamis 27 ga watan Yuli ana rike da Bazoum yayin wata hira da gidan talabijin na France 24 duk da ba a san inda ministan yake ba.
Birnin Naimey ya kasance shiru a safiyar Alhamis bayan rufe iyakar kasar da kuma saka dokar ta baci a birnin da sojojin suka yi, cewar Punch.
Magoya bayan Bazoum a ranar Laraba sun taru a birnin don nuna rashin jin dadin su da shirin sauya gwamnati inda daga bisani aka watsa su, cewar The Times.
Duk da ba a san waye daga cikin sojojin ya ke jagorantar kasar a yanzu ba, amma Janar Omar Tchiani shi ne shugaban masu tsaron Bazoum yayin da sanarwar kuma Kanal Amadou Abdrahman ne ya fitar.
ECOWAS Ba Zata Lamurci Juyin Mulki A Jamhuriyar Nijar Ba, Tinubu Ya Sha Alwashi
A wani labarin, shugaban kasashen ECOWAS, Bola Tinubu ya gargadi sojoji a Nahiyar Afirka akan juyin mulki.
Tinubu ya ce kungiyar kasashen ba za ta lamunci yunkurin juyin mulki da ake a kasar Niger ba da sauran kasashen Nahiyar Afirka ta Yamma.
Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa D. Olusegun wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Asali: Legit.ng