Shugaba Tinubu Na Ganawa Da Kungiyoyin Kwadago Na NLC Da TUC a Fadar Gwamnati

Shugaba Tinubu Na Ganawa Da Kungiyoyin Kwadago Na NLC Da TUC a Fadar Gwamnati

  • Kungiyoyin kwadago na ƙasa na wata ganawa da wakilan Gwamnatin Tarayya a fadar shugaban ƙasa
  • Hakan na zuwa ne a lokacin da ƙungiyoyin suka sha alwashin tsunduma yajin aiki muddun gwamnati ta kasa magance tsadar rayuwa da ake ciki
  • Kungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), ta bai wa mambobinta umarnin fara shirin tsunduma yajin aiki a sati mai kamawa

FCT, Abuja - A yanzu haka shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa a fadar Gwamnatin Tarayya.

An bayyana cewa ƙungiyoyin kwadago na NLC da TUC ne ke gani da wakilan Gwamnatin Tarayya a fadar shugaban ƙasa.

Wata majiya mai karfi ta bayyana hakan a wata hira da jaridar The Punch da yammacin Laraba, 26 ga watan Yuli.

Wakilan kungiyar kwadago na gani da Tinubu
Tinubu na ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa. Hoto: News in Naija
Asali: Facebook

A kan menene Tinubu ke ganawa da NLC da TUC? Karin bayani

Kara karanta wannan

Halin da Ake Ciki a Gidan Atiku Abubakar Bayan Kama 'Yan Ta'adda Suna Shirin Kai Hari, An Fara Ɗaukar Matakai

Majiyar ta bayyana cewa kwamitin sulhu da Shugaba Tinubu ya kafa ne ya kira taron gaggawar biyo bayan gargaɗin shiga yajin aiki da NLC ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoton Daily Trust, NLC ta zargi Shugaba Tinubu da jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali ta hanyar tsare-tsaren da gwamnatinsa ta zo da su, musamman ma batun cire tallafin man fetur.

Kungiyar ta ce 'yan Najeriya ba su ƙara samun kwanciyar hankali ba tun lokacin da Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu.

Kungiyar kwadago ta sanar da ranar da za ta tsunduma yajin aikin gama gari

Legit.ng a baya ta yi rahoto cewa kungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), ta sanar da cewa za ta tsunduma yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Ɓullo, NLC Ta Faɗi Ranar Shiga Yajin Aiki a Faɗin Najeriya, Ta Gindaya Wa Tinubu Sharaɗi

NLC dai ta buƙaci gwamnatin Shugaba Tinubu da ta yi gaggawar janye tsare-tsarenta da suka janyo tsadar rayuwar da ake fama da ita a Najeriya.

Kungiyar ta yi kira ga rassanta na jihohi, da sauran ƙwawayenta ƙungiyoyin ma'aikata da ma na fararen hula, da su fara shirin tsunduma yajin aiki muddun gwamnati ta ƙi yin abinda ya dace.

Kungiyar ma'aikata ta buƙaci a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N200,000

Legit.ng a kwanakin baya ta kawo muku rahoto cewa gamayyar ƙungiyar ma'aikata wato WAISER, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ƙara albashin ma'aikata zuwa naira 200,000.

Kwadinetan ƙungiyar, Amodu Isiaka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 20 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng