Gwamnan APC Ya Fadi Hikimar Shugaba Tinubu a Cire Tallafin Fetur Tun Ranar Farko
- Gwamnan jihar Ogun ya ce ba komai ya jawo aka cire tallafin fetur ba sai asara da cutar da ke cikinsa
- Dapo Abiodun ya nuna alherin da za a samu daga tashin farashin mai, ya zarce duk wani sharrinsa
- Idan da Bola Tinubu ya kara bata lokaci, Gwamna Abiodun ya ce za a cigaba da cutar ‘Yan Najeriya
Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya yi magana a game da janye tsarin tallafin man fetur da Bola Ahmed Tinubu ya yi tun a ranar rantsuwa.
Premium Times ta rahoto Gwamna Dapo Abiodun ya na cewa shugaban kasar ya zabi ya tashi farashin litar man fetur ne saboda ya san halin ‘yan Najeriya.
A cewar Gwamnan, da Bola Tinubu ya bata lokaci kafin ya dauki mataki, mutane za su gano yadda za su cigaba da amfana da tsarin da ya zama dole a soke.
Olusegun Obasanjo uba ne ga Abiodun
Abiodun ya yi wannan bayani ne a ranar Talata bayan wata ganawa da ya yi da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a garin Abeokuta a Ogun.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan ya kai ziyara zuwa dakin karatun Cif Obasanjo da safe, Vanguard ta ce ya dauki lokaci su na zantawa da mutumin da ya kira tamkar mahaifinsa.
Da yake zantawa da manema labarai bayan nan, Abiodun ya zama lauyan gwamnatin kasa.
Me Bola Tinubu ya hango?
"Mutane su na tambayar meyasa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai ari an kawo wasu matakai kafin ya aiwatar da tsarin nan ba.
Maganar gaskiya mun san kan mu; mu ‘Yan Najeriya ne. tun da aka sanar da lokacin janye tallafin, za mu yi ta cutar kan mu da kan mu.
Saboda haka ba abu mara kyau ba ne, sai a fara daukar matakin da ya kamata, komai rashin dadinsa."
- Dapo Abiodun
"Bayan wuya sai dadi" Inji Gwamna
A cewar Mai girma Gwamnan na jihar Ogun, gwamnatin tarayya ta na rasa Naira tiriliyan hudu a shekara saboda jama’a su iya sayen man fetur da araha.
Saboda haka Abiodun ya ce babu lokacin da ya dace ayi waje da wannan tsari irin yanzu.
Har kullum, Gwamnan ya ce bayan wuya sai dadi, ya na mai kira ga al’umma su yi hakuri da tashin farashin, ya kara da cewa amfaninsa ya fi sharrinsa yawa.
Rayuwa ta kara yin tsada
Masu kuka game da matsin lambar tattalin arziki su dakata, wani rahoto da mu ka samu kwanakin baya ya nuna cin kwa-kwa bai kare ba tukuna a Najeriya.
Bismarck Rewane ya ce sai an kai shekarar badi kafin gwamnati ta gane bakin zaren bayan farashin kudin kasashen waje ya tashi, sannan an cire tallafin fetur.
Asali: Legit.ng