Abba v Kwankwaso, Ahmadun Alu v Alu da Sauran Gwamnoni 4 Masu Uban Gida
- Rabiu Musa Kwankwaso (Kano), Aliyu Magatakarda Wamakko (Sokoto) sun kafa Gwamnatoci
- A kudancin Najeriya, ana ganin har yanzu Ifeanyi Okowa da Nyesom Wike su na rike da jihohinsu
- Yaran ‘yan siyasar nan su ke rike da Gwamnati, amma wasu na tunanin akwai masu juya su a gefe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Gwamnoni kusan hudu ake ganin sun yi amfani da iyayen gidansu wajen yin nasara a zaben 2023, ana zargin har yanzu su na da karfi a gwamnati.
Daily Trust ta ce ‘yan siyasar da suka kafa gwamnatoci su ne: Rabiu Musa Kwankwaso, Aliyu Magatakarda Wamakko, Ifeanyi Okowa da Nyesom Wike.
A zaben 2019 Abba Kabir Yusuf da Ahmad Aliyu su ka samu goyon iyayen gidansu, su ka yi takarar Gwamna a Kano da Sokoto, kuma saura kiris su kai labari.
Jihohin da ake da iyayen gida
1. Kano
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daf da zaben 2023, sai aka ji Rabiu Musa Kwankwaso ya bar PDP zuwa NNPP, nan take Abba Kabir Yusuf da dinbin magoya bayansa su ka sauya-sheka.
Ko da aka zo zabe, Abba Gida Gida da Aminu Abdussalam Gwarzo wanda duk sun yi aiki a karkashin Kwankwaso, su ka lashe zaben Gwamna a Jihar Kano.
Ana zargin Gwamnatin NNPP tamkar tsohon Gwamna Kwankwaso ne yake wa’adi na uku, musamman idan aka ji kalamansa da mukaman da aka nada.
A jerin Kwamishinoni, Legit.ng ta fahimci mutanen Kwankwaso su ka samu kujeru fiye da 10. Amma tsohon Gwamnan ya nuna bai rike da madafan iko.
2. Ribas
A Ribas kuwa, Nyesom Wike ya yi nasara wajen ganin ‘danuwansa watau Siminalayi Fubara mai shekara 44 da haihuwa ya gaje shi wajen zama Gwamna.
Ko da ya tashi nada Kwamishinoni, Simi Fubara ya dawo da mutane goma da su ka yi aiki da Wike, sannan ya bar SSG da shugaban ma’aikatan gidan gwamna.
3. Delta
A jihar Delta, tsohon Gwamna Ifeanyi Okowa ne ya shiga-ya fita har Sheriff Francis Orohwedor Oborevwori ya lashe zaben 2023 kuma ya zama Gwamna.
Rahoton ya ce ana yi wa Oborevwori kallon yaron Okowa. Gwamnan bai gama nada kwamishinoni ba, amma da alama sai yadda Okowa ya yi har gobe.
4. Sokoto
Goyon bayan Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya taimakawa Ahmed Aliyu wajen zama Gwamna a Sokoto, kafin yanzu ya rike Kwamishina a lokacinsa.
Tun kafin Wammako ya zama Gwamna ya samu kusanci da Aliyu. A 2019 ya zama mataimakin Gwamna, da Aminu Tambuwal ya koma PDP, ya yi zamansa a PDP.
Sabon Gwamnan bai nada Kwamishinoni ba, amma mutanen Wammako su ka samu mukaman da aka bada, zargin da wasu ke yi shi ne Alu zai rike madafan iko.
Nadin Ministocin Najeriya
A rahoton da mu ka fitar, an ji labari hukumomin DSS da EFCC da Majalisar Dattawa za su jawo mutanen Shugaba Bola Tinubu su gagara zama Ministocin tarayya.
Watakila wasu tsofaffin Gwamnonin APC su na ruwa a sakamakon samun su da tafka rashin gaskiya, amma kuma za a ba wasu daga jam’iyyun adawa mukamai.
Asali: Legit.ng