Sunayen Gwamnonin APC Da PDP Da Ake Zargi Da Rashin Cikakkun Takardun Kammala Karatu
- A yanzu haka akwai gwamnonin APC da na PDP da ake ƙalubalanta kan takardun karatunsu
- Batun takardun kammala karatu na daga cikin abubuwan da aka shigar da su ƙara a gaban kotu
- A can bayan manyan 'yan siyasa da dama sun rasa kujerunsu kan gaza gabatar da shaidar kammala karatu a sanda buƙata ta taso
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Da yawa daga cikin ‘yan siyasar Najeriya sun shiga cikin rigingimu na satifiket ɗin kammala karatu ko na bautar ƙasa, wanda hakan ya janyowa wasunsu rasa kujerunsu.
Misali, tsohuwar ministar kuɗi, Kemi Adeosun, wacce ta yi aiki a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta rasa muƙaminta saboda rashin gabatar da sahihin satifiket ɗin bautar kasa wato NYSC.
Haka nan, an kori jam’iyyar APC daga zaɓen gwamna na 2019 a jihar Bayelsa, lokacin da aka samu mataimakinsa da takardu na bogi.
A yanzu haka wasu gwamnonin APC da na PDP sun faɗa cikin irin wannan bahallatsa, kuma ana ta cece-kuce a kai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas
A yanzu haka Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, wanda ɗan APC ne, yana fuskantar shari'a a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe dangane da sakamakon jarabawar sa ta WAEC.
A ranar Laraba ne wata ƙungiya ta bai wa WAEC wa’adin sa’o’i 48 da su gabatar da sakamakon Sanwo-Olu ko kuma a yi ƙararsu.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan da ya gabatar da sakamakon jarabawarsa ta WAEC ga jama’a, domin tabbatar da adalci kamar yadda The Guardian ta wallafa.
Peter Mbah na Jihar Enugu
A nasa bangaren, gwamnan jihar Enugu na fama ne da rigimar satifiket ɗin NYSC a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke jihar Enugu.
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour ne ya shigar da ɗan takarar na PDP da ya lashe zaɓen ƙara a gaban kotu.
Hukumar ta NYSC ta ce satifiket ɗin da gwamnan ya bai wa hukumar zaɓe wato INEC, ba ita ce ta buga shi ba kamar yadda Sahara Reporters ta kawo.
Tinubu ya sa dokar ta ɓaci kan batun samar da abinci a Najeriya
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sanya dokar ta ɓaci kan batun samar da abinci a Najeriya.
Wannan duk yana cikin shirye-shiryen da gwamnatin Tinubu ke yi na ganin marasa ƙarfi sun samu sauƙin rayuwa.
Asali: Legit.ng