Sababbin Shugabannin Kwamitoci 8 Da Mataimakansu Da Aka Zaba a Majalisar Dattawa
- Godswill Akpabio ya sanar da Sanatocin da su ka samu shugabanci na kwamitoci na musamman
- Sababbin Sanatoci irinsu Shehu Buba Umar da Asuquo Ekpenyong sun yi dacen rike kwamiti
- Adeyemi Adaramodu da Sanatan Osun ta tsakiya, Salisu Afolabi sun zama Kakakin Sanatoci
Abuja - A zaman farko da majalisar tarayya tayi a makon nan aka kafa kwamitocin da za su jagoranci ayyukan Sanatoci a majalisar dattawa.
Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya bayyana cewa an sanar da shugabannin kwamitoci na musamman da kuma mataimakansu a majalisar.
An raba shugabancin ne tsakanin jam’iyyun APC, PDP da kuma SDP. Hakan ya nuna Sanata Godswill Akpabio zai tafi da ‘yan adawa mulkinsa.
Kamar yadda aka saba, Legit.ng Hausa ta fahimci an bar wa Sanatan Nasarawa, Aliu Wadada Ahmed (SDP) shugabancin kwamitin asusun gwamnati.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda aka yi rabon kujeru:
1. Harkokin majalisa — Titus Zam (Shugaban kwamiti), Opeyemi Bamidele (Mataimakin shugaban kwamiti)
2. Ayyukan majalisa — Sunday Karimi (Shugaban kwamiti), Williams Eteng Jonah (Mataimakin shugaban kwamiti)
3. Dokoki da korafin jama’a — Okechukwu Ezea (Shugaban kwamiti), Khalid Ibrahim Mustapha (Mataimakin shugaban kwamiti)
4. Asusun gwamnati — Aliu Wadada Ahmed (Shugaban kwamiti), Onyeka Peter (Mataimakin shugaban kwamiti)
5. Tsaron kasa— Shehu Buba Umar (Shugaban kwamiti), Asuquo Ekpenyong (Mataimakin shugaban kwamiti)
6. Bin ka’idar majalisa — Garba Musa Maidoki (Shugaban kwamiti), Ede Dafinone (Mataimakin shugaban kwamiti)
7. Yada labarai — Adeyemi Adaramodu (Shugaban kwamiti), Salisu Shuaibu Afolabi (Mataimakin shugaban kwamiti)
8. Kasafi — Olamilekan Adeola (Shugaban kwamiti), Ali Ndume (Mataimakin shugaban kwamiti)
Tsige Abdullahi Adamu
Rahoto ya zo cewa wasu su na so shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu ya sauka daga kujerarsa a NWC domin kawai a ba Kiristocin kasar nan dama.
Ganin Shugaban kasa (Bola Tinubu) da mataimakinsa (Kashim Shettima) duka musulmai ne, hakan ya jawowa Shugaban jam'iyyar APC na kasa cikas.
Asali: Legit.ng