Cikaken Sunaye: Masari, Abdulaziz, Rahman Sa Sauran Hadimai 17 Da Tinubu Ya Nada

Cikaken Sunaye: Masari, Abdulaziz, Rahman Sa Sauran Hadimai 17 Da Tinubu Ya Nada

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake nada masu ba shi shawara na musamman a bangarori da dama guda 20
  • Daga cikin mukaman akwai manyan masu ba shi shawara na musamman da masu daukar hoto da mai kula da lafiyarsa
  • Abdulaziz Abdulaziz da Tunde Rahman da kuma Ibrahim Masari na daga cikin wadanda suka samu shiga jerin nade-naden

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada mutane 20 a matsayin masu ba shi shawara na musamman.

Wannan na zuwa ne makwanni uku kacal bayan ya yi nade-naden mukamai a gwamnatinsa, cewar Premium Times.

Cikaken Sunaye: Masari, Abdulaziz, Rahman Sa Sauran Hadimai 17 Da Tinubu Ya Nada
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Da Wasu Daga Cikin Hadimansa. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Tinubu Rahman and O'tega Ogra.
Asali: Facebook

Sabbin nade-naden sun hada da manyan masu ba shi shawara na musamman (SSAs) da masu daukar hoto, mai kula da lafiyarsa, da kuma masu ba shi shawara (PAs), Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kujerar Shugaban APC Na Tangal-Tangal Bayan Wata 15, Zai San Makomarsa a NEC

Masari, Abdulaziz Rahman da sauran hadimai na Tinubu

Daga cikin wadanda suka samu shiga akwai Tunde Rahman (SSA) a yada labarai sai Abdulaziz Abdulaziz (SSA) da kuma Ibrahim Masari mai ba da shawara a harkar siyasa, TheNews Nigeria.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran sun hada da Adekunle Tinubu mai kula da lafiyarsa da Damilotun Aderemi a matsayin sakatare sai Demola Oshodi a bangaren tsare-tsare, sai kuma Tope Ajayi a bangaren harkokin jama'a.

Cikakken jerin sunayen wadanda aka nada mukamai daban-daban:

1. Dakta Adekunle Tinubu – Mai kulada lafiyar Shugaba Tinubu

2. Tunde Rahman – Mai ba da shawara na musamman a harkar yada labarai

3. Damilotun Aderemi – Mai ba da shawara na musamman (Sakatare mai zaman kansa)

4. Ibrahim Masari – Mai ba da shawara na musamman a harkar siyasa

5. Toyin Subair – Mai ba da shawara na musamman a harkokin cikin gida

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo Najeriya, Gbajabiamila da Ganduje Sun Tarbo Shi a Filin Jirgi

6. Abdulaziz Abdulaziz – Mai ba da shawara na musamman a harkar yada labarai (Na bugawa)

7. Demola Oshodi – Mai ba da shawara na musamman a kan tsare-tsare

8. Tope Ajayi – Mai ba da shawara na musamman a yada labarai da harkokin jama’a

9. Yetunde Sekoni – Mai ba da shawara na musamman

10. Motunrayo Jinadu – Mai ba da shawara na musamman

11. Segun Dada – Mai ba da shawara a kan kafafen yada labarai

12. Paul Adekanye – Mai ba da shawara a dabarbaru

13. Friday Soton – Mai ba da shawara a kula da gida

14. Shitta-Bey Akande – Mai ba da shawara a harkar abinci

15. Nosa Asemota – Mai ba da shawara a sadarwa na zamani, kuma mai daukar hoto

16. Kamal Yusuf – Mai ba da shawara a ayyuka na musamman

17. Wale Fadairo – Mai ba da shawara a ayyukan gama gari

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Bola Tinubu Ya Yi Sabin Nade-Nade 2 Masu Muhimmanci

18. Sunday Moses – Mai ba da shawara a harkar daukar faifan bidiyo

19. Taiwo Okanlawon – Mai ba da shawara a haukar hoto (Karami)

20. O’tega Ogra – Babban mai ba da shawara a kafar yada labarai ta zamani

Tinubu Ya Nada Ribadu, Darazu, Alake da Wasu 5 A Matsayin Ma Su Ba Shi Shawara

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade na masu ba shi shawara na musamman.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai yada labaransa ya fitar, Abiodun Oladunjoye a ranar Alhamis 15 ga watan Yuni.

Nade-naden sun hada da Mallam Nuhu Ribadu da Dele Alake da Yau Darazau da Salma Ibrahim Anas da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel