Jam’iyyar LP Ta Yi Azarɓaɓin Faɗin Abin Da Zai Faru a Ƙarshen Shari'ar Obi Da Tinubu
- Hukuncin da kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa za ta yanke shi ne a sake maimaita takara
- Julius Abure ya ce labari ya zo masu cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC sun fara shiri domin komawa filin zabe
- Shugaban jam’iyyar LP ya ankarar da magoya bayan Peter Obi cewa an hango take-taken kotun zabe
Abuja - Shugaban jam’iyyar LP ta kasa, Julius Abure yana neman yin karambani a game da shari’ar karar zaben shugaban kasa da ke gaban kotu.
Kamar yadda labari ya zo a Vanguard, Barista Julius Abure ya yi kira ga ‘yan jam’iyyarsu ta LP da su shiryawa mai-men zaben shugaban kasa.
A cewar Abure, ya samu labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki da kan ta, ta fara shirye-shirye kan maimaicin zaben da za a gudanar a Najeriya.
Shugaban LP na kasa ya bukaci magoya bayansu su kwana cikin shiri domin yin abin da ya kira a kara kunyata jam’iyyar APC da gwamnatinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar ta ce Abure ya bayyana wannan ne a wajen wani taro da ya yi ta yanar gizo da kungiyar hadin-gwiwar mutanen Najeriya da kasar Amurka.
A jiya ‘dan siyasar ya zanta da Farfesa Eddie Oparaoji wanda ke jagorantar kungiyar a Amurka kuma wanda ya yi mata kamfe a lokacin zaben 2023.
“Wadanda su ke gwamnati sun fara shiryawa mai-man zabe kuma wannan yana cikin goyon bayan da mu ke neman daga gare ku.
Dole mu ma mu fara shiryawa domin gudun wadanda su ke cikin gwamnati su mamaye mu.
Saboda haka za mu bukaci gudumuwarku a bangaren nan ko da an samu matsalar soke zaben wanda ba shi mu ke nema ba.
Abin da mu ke roko shi ne a ayyana Peter Obi a matsayin shugaban kasar Najeriya nan-take.
- Julius Abure
"Peter Obi ya ci zabe" - LP
Daily Trust da ta kawo labarin, ta ce shugaban na LP ya ce alkaluman da ke hannunsu sun tabbatar masu da cewa Peter Obi ne ya lashe zaben 2023.
Ko da ba a Obi nasara ba, jam’iyyar adawar ta na ganin cewa za su karbe mulkin Najeriya da zarar kotun zaben ta bukaci a maimata zaben shugaban kasa.
Tinubu zai nada Ministoci
A wani gefen, rahoto ya zo mana cewa sunayen wadanda za a tantance a matsayin Ministocin tarayya ya isa hannun jami'an hukumomin DSS da na EFCC.
An ce take-take na nuna masu ba shugaban kasa shawara za su fi Ministoci iko a mulkin Bola Tinubu, akasin abin da aka saba gani a sauran gwamnatoci.
Asali: Legit.ng