El-Rufai Ya Yi Magana Kan Kamun Ludayin Gwamnatin Tinubu

El-Rufai Ya Yi Magana Kan Kamun Ludayin Gwamnatin Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai ya shawarci Tinubu da ya nada mukamai wurin duba kwarewa ba wa ka sani ba
  • El-Rufai ya fadi haka ne a jiya Lahadi 9 ga watan Yuli yayin wani taro na kaddamar da littafin Farfesa Akintola a jami'ar Lagos
  • Ya bayyana yadda jihar Kaduna ta shiga matsanancin hali saboda yadda a baya a nada mukamai ba bisa ka'ida ba

Jihar Lagos - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-rufai ya ce gudanar da mulki don inganta rayuwar al'umma shi ya kamata a ba wa fifiko don ci gaban kasa.

Elrufai ta bayyana haka a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli yayin kaddamar da littafin tarihin rayuwar Farfesa Ishaq Akintola a jami'ar Lagos.

El-Rufai Ya Yi Magana Kan Kamun Ludayin Gwamnatin Tinubu
Tsohon Gwamna, Nasir El-Rufai Da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Nasir El-Rufai/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Farfesan ya yi ritaya a jami'ar bayan cika shekaru 70 ya na aiki, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Alhazan Kano 9 Sun Barke Da Gudawa A Makkah Bayan Gama Aikin Hajji, Dalili Ya Bayyana

El-rufai ya ce kamun ludayin Tinubu zai kawo sauyi a kasar

Elrufai wanda ya karbi lambar yabo a taron, ya ce Tinubu ya na kan hanya madaidaiciya ganin irin matakan da yake dauka a yanzu, Peoples Gazette ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Yadda wannan gwamnati ke sauya al'amura don inganta rayuwar talakawa a kankanin lokaci ya tabbatar da cewa dole mu rinka nada mukamai akan kwarewa ba wa ka sani ba.
"Dole mu kawar da bambancin addini ko kabilanci a gudanar da mulki inda ba za a nuna wa kowa wariya ba a kasa.
"Dukkan mu mun fito daga manyan addinai guda biyu, idan an bamu mukamai ya kamata kuyi koyi da koyarwar addinin Musulunci da Kiristanci."

Ya ce duka addinai guda biyu na kasar na koyar da shugabanci na gari

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

Ya kara da cewa:

"Addinan guda biyu suna koyar da shugabanci na gari, amma wadansu suna yin ganin damansu ba tare da koyi da addinan ba."

El-Rufai ya ce yadda ake nada mukamai a baya ba tare da bin kwarewa ba, shi ya jefa jihar Kaduna cikin matsanancin halin da take ciki, cewar TheCable.

An Ja Kunnen Bola Tinubu Kan Yaudarar Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai

A wani labarin, wani dan rajin kare hakkin dan Adam ya gargadi Bola Tinubu kan yaudarar Nasir El-Rufai.

Deji Adeyanju ya ce dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu ya shirya tsaf don fuskantar yaudara daga Nasir El-Rufai.

Adeyanju ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya ce Tinubu ya bi a hankali saboda mulki babu tabbas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.