An Ja Kunnen Tinubu Kan Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

An Ja Kunnen Tinubu Kan Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

  • An ja kunnen ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, akan gwamnan jihar Kaduna
  • Wani ɗan gwagwarmaya a harkar siyasa shine ya gargaɗi Tinubu kan El-Rufai
  • Deji Adeyanju yace El-Rufai butulu ne domin yaci amanar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Wani ɗan rajin gwagwarya mai suna Deji Adeyanju, yayi wani muhimmin gargaɗi ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Deji Adeyanju ya gargaɗi Tinubu kan cewa ya shirya tsaf domin fuskantar yaudara daga gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai. Rahoton Tribune

Tinubu
An Ja Kunnen Tinubu Kan Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Asali: Depositphotos

Adeyanju yayi wannan gargaɗin ne a ranar Asabar a wani rubutu da yayi a shafin sa na Twitter, inda yace Tinubu yabi a hankali domin mulki abu ne mai shuɗewa.

A cewar sa gwamnan na jihar Kaduna ya yiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, butulci.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Kotun ƙoli ta Yanke Na Canjin Fasalin Kuɗi Zai Kasance Kyakkyawan Tushe Ga Mulkin Tinubu — Yahaya Bello

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“El-Rufai zai ci amanar Tinubu a lokacin da ya dace. Shugaba Buhari yana ganin sabon darasi yanzu. Tun kafin ya bar kujerar mulki har sun fara gasa masa gyada a hannu. Lallai mulki baya da tabbas."

Gwamna El-Rufai, na hannun daman shugaba Buhari ne, wanda suka kwashe kusan shekara bakwai da rabi suna tafiya a kan turba guda tare.

Sai dai a cikin ƴan kwanakin nan Gwamnan da takwaran sa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sun raba gari da shugaban ƙasar akan rigimar sauyin takardun kuɗin naira. Rahoton Daily Post

Gwamnonin biyu sun fito fili sun caccaki shugaban ƙasar kan matsayar sa a game da lamarin sauyin kuɗin da aka yi a ƙasar nan.

Nasir El-Rufai da Ganduje ƙiri-ƙiri suka fito suka nunawa duniya basa tare da shugaba Buhari, inda suka nemi mutanen jihohin su da suyi fatali da umurnin shugaban ƙasar na daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na N500 da N1000

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kama Ɗan Majalisar Tarayya Na NNPP da Bindiga a Kano

Kayi Mana Komai a Borno, Dole Mu Zaɓe Ka -Zulum Ga Tinubu

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Borno ya yiwa ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu wani muhimmin alƙawari.

Gwamna Zulum yace yanzu lokaci na rama biki ga Tinubu bisa wani muhimmin taimako da ya yiwa jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel