Kotu Ta Kawowa Shugabannin APC Cikas, Ta Tabbatar da Korar Sanata Daga Jam’iyya

Kotu Ta Kawowa Shugabannin APC Cikas, Ta Tabbatar da Korar Sanata Daga Jam’iyya

  • Kotun tarayya da ke garin Abuja ta yi hukunci a shari’ar Mohammed Danjuma Goje da Jam’iyyar APC
  • Alkali Obiora Egwuatu ya ce shugabannin APC na Gombe ba su saba doka wajen korar Sanatan na su ba
  • Hukuncin ya zama daidai da matakin da aka dauka a Gombe, ya sabawa matakin da APC NWC ta dauka

Abuja - Alkalin kotun tarayya mai zama a garin Abuja, Obiora Egwuatu, ya saurari karar da Mohammed Danjuma Goje ya shigar tsakaninsa da APC.

Leadership ta ce Sanata Mohammed Danjuma Goje ya na kalubalantar shugabannin jam’iyyar APC na reshen Kashere a jihar Gombe da su ka kore shi.

Hakan yana zuwa ne bayan dakatar da tsohon gwamnan daga jam’iyya mai-ci, daga baya sai shugabannin APC su ka yanke shawarar fatattakar shi.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

'Yan APC
Adamu, Buni, Inuwa, Goje a taron sulhun APC Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: UGC

Laifin Danjuma Goje ne

Danjuma Goje bai gamsu da matakin da shugabannin mazabarsa su ka dauka ba, saboda haka ya shigar da kara a kotun tarayya domin a wanke shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da ya saurari karar jiya, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya zartar da cewa Sanata Goje ya san da zargin da ke kan shi, kuma an nemi ya kare kan shi.

Alkalin yace ‘dan majalisar ya ki zama gaban kwamitin da aka kafa domin wanke kan shi.

Rahoto ya kara da cewa a karshe Egwuatu ya yi fatali da bukatar Sanatan na Gombe ta tsakiya, ya jaddada matsayar da APC ta dauka na korar sa daga cikinta.

Goje wanda ya yi Gwamna a jihar Gombe tsakanin 2003 da 2011 bai iya gamsar da kotun tarayyar cewa an saba dokar kasa wajen korar shi daga jam’iyya ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fuskanci Barazana, Lauyoyi 8 Za Su Kai Shi Kotu Kan Harajin Abin Hawa

Jam'iyyar APC ta yi farin ciki

Su kuwa shugabannin jam’iyyar ta APC a jihar Gombe sun ji dadin hukuncin, su ka jinjinawa Alkalin kotun tarayyar ganin an dauki matakin ladabtarwa.

APC ta ce hukuncin da aka zartar ya nuna karfin da shugabannin jam’iyya su ke da ita a doka.

Alamu sun nuna APC ta na tare da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, (Dan-Majen Gombe), tayi kira ga Goje ya rungumi kaddarar da auka masa.

“Kul aka nada barayi a Gwamnati”

A rahoton da mu ka fitar a dazu, an ji Sanata Shehu Sani ya ce kyau gwamnati ta cafke tsofaffin Gwamnonin da su ka bar jiharsu cikin talauci da bashi.

‘Dan siyasar yake cewa ba zai zama daidai ayi tunanin bada mukamai ga tsofaffin Gwamnoni ko Ministocin tarayya da su ka sace dukiyar al’ummarsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng