Jagororin APC Sun Hakura, Sun Yarda Bola Tinubu Ya Nada Wike a Matsayin Minista
- Kungiyar Amalgamated Bola Tinubu Campaign Council a jihar Ribas ta jinjinawa Nyesom Wike
- Tony Okocha wanda yake jagorantar kungiyar ya ce tsohon Gwamnan ya taimaki APC a 2023
- Ganin gudumuwar da ya ba Bola Tinubu a zaben da ya wuce, Okocha sun gamsu a ba Wike Minista
Rivers - Mafi yawan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC ta reshen jihar Ribas, sun yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya nada Nyesom Wike ya zama Minista.
A rahoton The Nation aka ji jagororin jam’iyyar ta APC mai mulkin kasar nan su na ganin tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya cancanci kujera a FEC.
‘Yan majalisar Amalgamated Bola Tinubu Campaign Council da su ka yi wa APC kamfe a jihar Ribas sun ce ‘dan siyasar ya ba su gudumuwa a zaben 2023.
Tony Okocha ya soki Magnus Abe
Cif Tony Okocha wanda shi ne shugaban wannan tafiya, ya caccaki ‘yan siyasa irinsu Sanata Magnus Abe da ya ce su na neman fada a mulkin Bola Tinubu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jigon na jam’iyyar APC ya ce Abe ya bar su ne a lokacin da ake bukatarsa, sai daga baya ya dawo ya na neman sabon shugaban kasan ya rika damawa da shi.
Kamar yadda Vanguard ta rahoto, Okocha ya ce Wike a lokacin ya na Gwamna ne ya taimaki Bola Tinubu bayan duka jiga-jigan su sun juya masu baya a zabe.
"A lokacin da (Rotimi) Amaechi ya tafi, Magnus (Abe) ya tafi, babu wanda ya rage sai mu da kuma wasu ‘yan tsirarun kungiyoyin magoya bayanmu.
Tun daga 1999, PDP ke da iko da Ribas, Ko a 2015 lokacin da na ke shugaban fadar gwamnati, Amaechi ya na Gwamna, kuri’u 69, 000 APC ta samu.
A 2015, jam’iyyar PDP ta samu kuri’u kusan miliyan biyu, kuma mu ne da mulki, sannan (Amaechi) yana Darekta Janar na yakin zaben Buhari.
A 2019 da Wike ya zama Gwamna, abin ya kara muni. A zaben 2015, APC ta samu 7%, sai a 2019 mu ka samu 5%, sai ga APC tayi nasara a 2023."
- Tony Okocha
Ya aka yi Tinubu ya kawo Ribas?
Okocha ya ce ba kowa ya yi wannan aiki na hana PDP nasara a zaben shugaban kasa ba illa Wike, ya biya wakilan APC a duka rumfuna 6, 868 da ke jihar Ribas.
Babu mamaki tsohon Gwamnan ya samu kujerar Ministan Tarayya a gwamnatin APC.
A jihar Kano, an samu labari Ahmadu Haruna Danzago wanda ya na cikin jagororin APC da su ka yaki Dr. Abdullahi Ganduje ya zama shugaban REMASAB.
Sanusi Sirajo Kwankwaso ya zama mai ba Gwamnan Kano shawara kan siyasa. Wadanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada za su fara aiki a nan take.
Asali: Legit.ng